FASAHATechnology
Ƙarfafa al'umma da ilimin fasahar zamani
Digital Skills Training | AI Solutions | IT Consulting | Education & Business Digital Transformation Services
13/09/2026
Daga koyon fasahar zamani zuwa samun damarmakin ayyuka
💻 FASAHA Technology
''ƙarfafa al'ummar jahar Maradi da ilimin fasahar zamani''
A yau, sanin amfani da fasahar zamani ba kawai wata ƙwarewa ba ce,wata hanya ce ta samun damar aiki, fara sana'a da samar da mafita ga al'umma.
FASAHA Technology mun samar da tsarin horo na musamman domin taimaka wa matasa a jahar Maradi su koyi fasahar zamani cikin hanya mai kyau tare aikace-aikace.
🔄 HANYAR HORONMU
📚 1. KOYO — LEARN
Samun ingantaccen tushe a fannin fasahar zamani (Digital Skills).
🛠️ 2. AIKI DA ABIN DA KA KOYA — PRACTICE
Yin ayyuka na zahiri domin samun kwarewa da gogewa a tare.
💡 3. GINAWA — BUILD
Ƙirƙirar digital products, services da sabbin hanyoyin magance matsaloli.
💼 4. AIKI — WORK
Shiryawa domin samun aikin yi, freelancing, remote work da sauran damar sana'o'in zamani.
🚀 5. ƘIRƘIRA — CREATE
Fara sabbin sana'o'i da kasuwanci da s**a dogara da fasahar zamani.
🌍 6. TASIRI — IMPACT
Amfani da fasaha wajen magance matsalolin al'umma dan samar da ci gaba a jahar Maradi.
🎯 ABUBUWAN DA MUKE KOYARWA
💻 Computer & Digital Literacy
🎨 Graphic Design
📢 Digital Marketing
🌐 Web Design & Development
🤖 Artificial Intelligence & AI Tools
📱 Social Media Management
🎥 Content Creation
💼 Digital Entrepreneurship
🌍 Freelancing & Remote Work
🎓 EdTech & Digital Education
🏢 Business Technology Solutions
📊 Digital Productivity & Office Tools
💡 MANUFARMU BA KOYARWA KAWAI BA CE
Manufarmu ita ce mayar da ƙwarewar matashi zuwa damar aiki da gaske.
➡️ Aikin yi: Digital Skills → Kwarewa → Damar aiki
➡️ Freelancing: Digital Skills → Portfolio → Clients → Income
➡️ Kasuwanci: Digital Skills → Ra'ayi → Digital Service/Product → Sana'a
🌍 FASAHA TECHNOLOGY DA CI GABAN AL'UMMA
Muna ƙarfafa matasa su yi amfani da fasaha wajen:
✅ Taimaka wa ƙananan 'yan kasuwa su shiga duniyar dijital
✅ Inganta koyarwa da ilimi ta hanyar fasahar zamani
✅ Taimaka wa 'yan kasuwa wajen tallata hajarsu a yanar gizo
✅ Ƙirƙirar digital content ga businesses da organizations
✅ Ƙirƙirar sabbin hanyoyin magance matsalolin al'umma
✅ Koyar da wasu matasa dabarun fasahar zamani
✅ Ƙirƙirar sabbin sana'o'i da ayyukan da s**a shafi fasaha
🔥 MANUFAR MU:
Gina matasa masu ƙwarewa → Ƙarin damar aiki → Sabbin sana'o'i → Al'umma mai amfani da fasaha.
📍 Tessaoua,Maradi, Niger
Ka koyi fasahar zamani.
ka gina kwarewa.
ka ƙirƙiri dama.
ka fara sana'a.
Mu magance matsalolin al'umma ta amfani da fasahar zamani.
Email: [email protected]
WhatsApp Business+227 89184060
fasaha technology ''ƙarfafa al'ummar jahar Maradi da ilimin fasahar zamani''
08/09/2026
fasahar zamani tana tare damu,mi yasa ba zamu riƙa tattaunawa akan ta ba?
FASAHA Technology ''ƙarfafa al'ummar jahar Maradi da ilimin fasahar zamani''
A yau, fasahar zamani tana canza yadda muke koyo, kasuwanci, sadarwa, aiki da kuma gudanar da rayuwarmu.
Amma tambayar ita ce:
Shin al’ummarmu tana samun isasshen bayani game da wannan sauyi?
Me ya sa yake da muhimmanci mu riƙa tattaunawa kan fasahar zamani?
Fasaha ba ta tsaya ga masu karatun Computer Science ko Programming kawai ba.
A yau tana cikin ilimi, noma, lafiya, kasuwanci, banki da harkokin kuɗi, sadarwa, aikin gwamnati, kafafen yaɗa labarai da harkokin yau da kullum.
Misali, ƙaramin ɗan kasuwa a Maradi zai iya amfani da WhatsApp Business, Digital Marketing da E-commerce domin samun sababbin kwastomomi.
Ɗalibi zai iya amfani da Internet, Online Learning da AI wajen ƙara fahimtar karatunsa.
Matashi zai iya koyon Programming, Graphic Design, Cybersecurity, Data, Content Creation ko Freelancing ya samar wa kansa wata hanyar samun aiki ko kuɗin shiga.
Amma kafin mu amfana da waɗannan damammaki, muna buƙatar ilimi da tattaunawa.
Fasaha tana canzawa cikin sauri
Abin da yake sabo a yau na iya zama tsohon abu gobe.
AI na ci gaba da canzawa. Hanyoyin kasuwanci suna sauyawa. Ayyukan da ake yi da hannu ana samun hanyoyin yin su ta Digital.
Saboda haka, bai kamata mu koyi fasaha sau ɗaya kawai mu tsaya ba.
Ya kamata mu ci gaba da tambaya, tattaunawa, koyo da gwaji.
Gare mu Harshen Hausa na da muhimmiyar rawa
Ba kowa ne yake iya fahimtar bayanan fasaha cikin Turanci ko Faransanci ba.
Idan muka tattauna akan AI, Digital Skills, Cybersecurity, E-commerce da Digital Transformation cikin harshen Hausa mai sauƙi, za mu taimaka wa mutane da yawa su fahimci abin da ke faruwa a duniyar fasaha.
Hausa na iya zama harshen wayar da kai kan fasahar zamani.
Daga masu amfani zuwa masu ƙirƙira
Muna son matasan Maradi da na yankin Hausa su daina kallon kansu a matsayin masu amfani da fasaha kawai.
Mu koyi yadda za mu ƙirƙiri mafita da fasaha.
Wace matsala ce ke cikin makarantar ku?
Wace matsala ce ’yan kasuwa ke fuskanta?
Wace matsala ce manoma ke fuskanta?
Wace matsala ce al’umma ke fuskanta?
Wataƙila akwai hanyar fasaha da za ta taimaka wajen magance ta.
Muna da matasa masu basira, ra'ayoyi da ƙwazo. Abin da muke buƙata shi ne ilimi, dama, haɗin kai da muhalli na tattaunawa.
Yanzu muna son jin ra’ayinku:
1. Wace fasahar zamani kuke ganin ya kamata matasan Maradi su fi koya?
2. AI: dama ce, barazana ce, ko duka biyun?
3. Wace matsala ce a al’ummarku kuke ganin fasaha za ta iya taimakawa wajen magancewa?
4. Ya kamata mu ƙara yawan koyar da Digital Skills cikin harshen Hausa?
5. Wace fasaha kuke son mu fara tattaunawa a kai a DANDALIN FASAHAR ZAMANI?
Ku rubuta ra’ayinku a comment.
Ku SHARE wannan saƙo domin ya isa ga matasa masu sha’awar fasaha da yawa.
Ku TAG Ga abokin ku wanda yake cikin Tech ko yake son koyon fasahar zamani.
Ku FOLLOW FASAHA Technology domin samun ƙarin ilimi, wayar da kai da tattaunawa kan fasahar zamani.
Fasahar zamani ba ta nesa da mu. Mu ma muna da damar koyanta, amfani da ita, da ƙirƙirar namu hanyoyin magance matsalolin al’ummarmu.
FASAHA Technology
ƙarfafa al'ummar jahar Maradi da ilimin fasahar zamani.
06/09/2026
💬 Dialoguer
💡 Exposer
🤝 Connecter
🌍 Rencontrer
📈 Investir
Entrepreneurs, investisseurs, institutions, partenaires et acteurs de l’innovation : préparez-vous.
📍 Niamey, Niger
📅 Octobre 2026
BUSINEX 2026 — Business Innovation & Network Exchange.
Coming this October. 🔥
06/09/2026
💪🔥 OBJECTIF 2030 !
On avance, on apprend, on construit et on ne lâche rien. 🚀🇳🇪
06/09/2026
FASAHA Technology
05/09/2026
💻 DIGITAL SKILLS FLOWSHIP 3 TESSAOUA
FasahaTechnology
‘’ƙarfafa al'ummar jahar Maradi da ilimin fasahar zamani''
FASAHA Technology zamu fara wani sabon shiri na musamman domin ƙarfafa matasan garin Tessaoua da ilimin fasahar zamani. 💻🌍
A yau, fasahar zamani ba abin jin daɗi kawai ba ce , kayan aiki ne,wajen samun ilimi, aiki, kasuwanci da samar da sabbin damar samun kuɗi ce.
Shi ya sa muka ƙirƙiri DIGITAL SKILLS FLOWSHIP3 TESSAOUA, domin ba wa matasa da sauran masu sha’awar fasaha damar koyon muhimman dabarun da za su taimaka musu a rayuwa da kasuwanci.
🎯 ME ZA KA KOYA?
A cikin wannan shirin za mu mayar da hankali kan:
Basic Digital Skills
Koyon amfani da computer, wayar hannu da muhimman kayan aikin zamani.
🌐 Internet & Online Skills
Yadda ake amfani da Internet yadda ya dace domin neman ilimi, aiki, kasuwanci da sadarwa.
🤖 Digital Creativity & AI
Koyon yadda za ka yi amfani da Artificial Intelligence (AI) da sauran kayan aikin dijital wajen ƙirƙirar abubuwa da haɓaka aikinka.
💼 Digital Economy & Entrepreneurship
Yadda fasahar zamani za ta taimaka maka wajen fara ko bunƙasa kasuwanci, samun kwastomomi da shiga cikin Digital Economy.
👥 Mutanen da muke buƙata
Shirin ya dace da:
✅ Matasa
✅ Dalibai
✅ ‘Yan kasuwa
✅ Masu neman aiki
✅ Masu son zama freelancers
✅ Masu son koyon Computer
✅ Duk wanda yake son fahimtar AI da fasahar zamani
📌 Wuri: École Sud 2, Tessaoua
📞 WhatsApp/Phone: +227 89630458
📧 Email: [email protected]
🌍 MANUFARMU
FASAHA Technology tana aiki ne domin:
“ƙarfafa al’ummar Jihar Maradi da ilimin fasahar zamani.”
Muna son ganin matasa da al’ummar Maradi suna amfani da Computer, Internet, AI da Digital Skills wajen samun ilimi, ƙirƙirar ayyukan yi, bunƙasa kasuwanci da gina makoma mai kyau.
Kada ka tsaya kallon duniya tana canzawa , ka koyi yadda za ka kasance cikin masu jagorantar wannan canjin.
👉 Ka yi rajista yau domin ka kasance cikin DIGITAL SKILLS FLOWSHIP TESSAOUA
📲 Tuntuɓe mu ta WhatsApp: +227 89630458
FASAHA Technology Facebook Marketing
FACEBOOK MARKETING DAMAR HAƁAKA KASUWANCI!
A yau, kasuwanci bai tsaya ba kan shago kawai ba.
Da Digital Transformation, za ka iya kai kasuwancinka ga kwastomomi a Maradi, Nijar da ma duniya baki ɗaya.
FASAHA Technology na taimaka wa SMEs da ’yan kasuwa wajen:
✅ Facebook & Digital Marketing
✅ WhatsApp Business
✅ E-commerce & Website
✅ AI & Digital Tools
✅ Digital Skills & Business Transformation
💡 Ka daina amfani da fasaha don hira kawai,ka fara amfani da ita wajen bunƙasa kasuwancinka.
FASAHA Technology
Ƙarfafa al’ummar Maradi da ilimin fasahar zamani.
📧 "[email protected]" (mailto:[email protected])
📲 WhatsApp: +227 89184060
👉 Kalli bidiyon, Like ❤️, Share 🔄 kuma ka bi shafinmu domin ƙarin ilimin Digital Transformation.
Catégorie
Site Web
Adresse
Notifications
Soyez le premier à savoir et laissez-nous vous envoyer un courriel lorsque FASAHATechnology publie des nouvelles et des promotions. Votre adresse e-mail ne sera pas utilisée à d'autres fins, et vous pouvez vous désabonner à tout moment.