HR Reporters

HR Reporters

Share

HR Reporters: Is a media organisation that reports on the suppression or violation of rights.

If you notice any oppression, violation, harassment, or injustice, we need you to send us the report along with full details and solid evidence 🧾 to WhatsApp No

10/09/2026

Wata kotu da ke N’Djamena babban birnin Chadi, ta yanke wa tsohon jagoran ƙungiyar ƴan tawayen FDPC Abdoulaye Miskine, hukuncin ɗaurin shekaru 15 a gidan yari.

📷 HR Reporters

✓Follow, Share, And Subscribe =>

10/09/2026

Shugaban Amurka Donald Trump, ya ce zai bai wa Amurkawa dala 5,000 idan jam'iyyarsa ta Republican ta samu rinjaye a zaben tsakiyar wa'adi da zai gudana a watan Nuwamba. Sai dai shugaban bai bayyana inda za a samo kudin ba.

📷 HR Reporters

✓Follow, Share, And Subscribe =>

10/09/2026

Aƙalla ɗansanda guda ya mutu, yayin da akayi garkuwa da malaman makaranta biyar a ƙasar K**aru, bayan wani hari da ƴan aware s**a kai cibiyar horos da malamai a yankin arewa maso yammacin ƙasar da ake amfani da turancin Inglishi.

10/09/2026

Irin Nasarorin Da Aka Samu A Bangaren Tsaro

09/09/2026

Kunga Irin ta. Haka suke yaudarar.

Allah Ya sa wannan, ya zama darasi ga waÉ—an da suke da irin wannan tunanin

09/09/2026

Wata Mace dake cikin halin tsananin zafin naquda wato "labor pain" a wani asibiti da aka sakaya sunansa.... ta nemi da a kira mata mijinta ya shigo inda take akwai saƙon da zata fadamasa....

Sai de shigowar mijin keda wuya, yayin da ya duƙa da kunnensa domin sauraren bayanin da zata raɗa masa a kunne... Sai aka ga matar tai wuf ta cafki kunnen nasa tare da riƙesa gam tana jaaaa tare da kai duka tana kwarmato, wanda ke nuna alamar azabar naquda, ƙorafi da gargaɗi 'n kar a kuma...!😊

A karshe de da ƙyar ma'aikatan jinya da unguwa zoma s**a taru s**a ɓambare hannunta daga kunne mutum, ya sha zaba shima, nan aka barshi dafe da kunne ya zuba domin ta karcesa.

Toh Allah shi kyauta, Haihuwa ba sauƙi. Laifinsa shine yin Cikin 😅😅 don haka duk wanda matarsa a labor tace ace yazo karka shiga, kace tai maganarta da ma'aikatan labor room

ba lallai labarin yaxama gaskiyaba

Photos from HR Reporters's post 09/09/2026

Sojoji Sun K**a Mutane 2 Da Ake Zargi Da Kai Wa 'Yan Ta'adda Kayan Aiki A Yobe

Sojojin rundunar Operation HADIN KAI sun k**a mutane biyu da ake zargi da samar da kayan aiki ga 'yan ta'adda, inda s**a kwato dumbin kayan gyaran babura da ake zargin ana shirin kai wa mayakan Boko Haram da ISWAP da ke fadin yankin Yunusari-Mobbar a Jihar Yobe.

An k**a wadanda ake zargin ne a ranar Talata, 8 ga Satumba, 2026, bayan da sojojin s**a sami sahihan bayanan sirri game da zirga-zirgar kayayyakin da ake zargin na 'yan ta'adda ne.

Sak**akon samun wannan bayani, sojojin bataliya ta 159 da ke karkashin Sashi na 2 na rundunar Operation HADIN KAI, tare da sauran jami’an tsaro, sun tare kayayyakin a gadar Gumsa da ke Karamar Hukumar Geidam.

Kayayyakin da aka kwato sun hada da: tayoyin babura, crankshafts, oil seals, wayoyi (cables), bearings, kayan birki, gaskets, piston kits, sarkoki da sprockets, mita (speedometers), clutch plates, rocker arms, na'urar CDI, coils, rectifiers, da sauran kayan gyaran babura.

Haka kuma, sojojin sun kwato takalma guda 145 da kuma wayoyin salula na Tecno Android guda biyu, da sauran kayayyaki.

An mika wadanda ake zargin da kayayyakin da aka k**a ga rundunar leken asiri ta soja ta 27 (27 Military Intelligence Regiment) domin gudanar da bincike na gaba da kuma daukar matakin da ya dace.

Rundunar hadin gwiwar ta bayyana cewa wannan samame na daya daga cikin kokarin da ake yi na dakile hanyoyin samar da kayan aiki ga 'yan ta'adda, da kuma hana Boko Haram da ISWAP samun kayayyakin da suke bukata domin ci gaba da ayyukansu.

Ta kuma yi kira ga mambobin kungiyoyin jama'a da su ci gaba da bai wa hukumomin tsaro sahihan bayanai akan lokaci.

📷 HR Reporters

✓Follow, Share, And Subscribe =>

Photos from HR Reporters's post 09/09/2026

SOJOJIN SASHIN "OPERATION FANSAN YAMMA" SUN CETI MUTANE 12 WADANDA AKA SACE, SUN KUMA DAKILE YUROWAR GARKUWA DA MUTANE A JIHAR ZAMFARA

Sojojin Hadin Gwiwa na Shiyyar Arewa maso Yamma karkashin rukunoni na Biyu (Sector 2 Joint Task Force North West), na rundunar Operation FANSAN YAMMA, sun ceti farar hula mutane 12 yayin wasu samame daban-daban da s**a kai kan 'yan ta'adda a kananan hukumomin Kaura Namoda da Tsafe da ke Jihar Zamfara a ranar 7 ga watan Satumba, 2026.

A lamari na farko, sojojin sun garzaya bayan sun sami kiran gaggawa na neman dauki sak**akon shigar wasu 'yan ta'adda cikin wani gida a garin Tsohon Tasha, da ke Karamar Hukumar Kaura Namoda. Jami'an tsaron sun yi fito-na-fito da 'yan ta'addan, lamarin da ya tilasta musu barin farar hula mutum shida da s**a yi garkuwa da su, sannan s**a tsere ta wani kogi da ke kusa. Daga baya an kwashe mutanen da aka ceton aka kuma sake hada su da iyalansu.

08/09/2026

To Allah Ya Sawake. Ita Gaskiya Guda ce

08/09/2026

''Duk da Musulunci ya bayar da damar mai idda ta fita da rana, akwai cikakken hani game da batun yin balaguro a lokacin da mace ke cikin idda''.

Want your business to be the top-listed Media Company in Abuja?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Address

No. 48 Aku Street Zuma Rock Abuja
Abuja

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when HR Reporters posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Subscribe

We will notify you when anything happens in Abuja.