HG Autoreviews

HG Autoreviews

Share

We open this page to share our knowledge on vehicles. We review any type of cars from any car brands

Photos from HG Autoreviews's post 10/06/2026

Idan kanada kudin sayen daya daga cikin wadannan motocin wacce zaka saye kuma meye dalili?

30/05/2026

Duka wadannan motocin suna a MID-SIZE car category ne.

Wannan motar ta sama CAMRY qirar 7th generation (VX50) ce wadda aka fara qera ta a 2012 -2017 amma wannan hoton camry din daga 2012-2014 ne kadai ake Samun wannan body style din, kafin facelift. Seventh generation sunzo da ijina uku kacal (three engine options only) gasu Kamara haka
2.5L 2AR-FE DOHC four cylinder engine wanda yakeda qarfin doki 178 da kuma qarfin torque 170 (178 horsepower and 170 pound feet of torque).
3.5L 2GR-FE DOHC six cylinder V6 engine wanda keda qarfin doki 268 da qarfin torque 248 (268 horsepower and 248 pound feet of torque).
2.5L HYBRID four cylinder engine wanda keda qarfin doki 200 (200 horsepower)

Motar da ke qasa ACCORD qirar 9th generation (CR2-CR3) ce kuma an fara qera wannan body style din daga 2013-2017 amma wannan hoton daga 2013-2015 ne kadai ake samunta kafin ayi facelift. Nine generation suma sunzo da ijina shida ne ( sxi engine option) amma biyu daga cikin shida din HYBRID engines ne. Inijinan gasu Kamara haka
2.4L DOHC i-VTECH K24 four cylinder engine wanda Yazo da fasahar direct injection da CVT automatic , injin din yanada qarfin doki 185 da qarfin torque 189 ( 185 horsepower and 189 pound feet of torque)
2.4L DOHC i-VTECH K24 four cylinder engine shima yazo da fasahar direct injection da six speed manual transmission da kuma CVT automatic transmission
3.5L SOHC i-VTECH V6 J35Y1 six cylinder engine wanda shima yazo fasahar direct injection da six speed manual transmission da kuma six speed automatic transmission. V6 din yanada qarfin doki 278 da qarfin torque 252

Kamar yadda na fada ACCORD tanada HYBRID da kuma plug in HYBRID kamar haka
2.0L DOHC i-VTECH four cylinder engine duka hybrid engines din sunzo da qarfin doki 196 da qarfin torque 226( 196 horsepower and 226 pound feet of torque) kawai banbancinsu shine plug in hybrid tafi babban battery kuma ana laqa mata caji kamar yadda ake laqa wayar hannu.

Dukda cewa accord tafi camry manyan injina a horsepower da torque kuma abun mamaki sunfi injinan camry qarancin shan mai (fuel economy) sannan kuma accord tafi camry quality interior da kuma luxury. Amma ba anan gizo ke sakar ba.
Camry tafi accord aminci duk da cewa tazarar ba me tsawo bace kuma tafi accord second-hand value (resell value).
Abinda mutane ya kamata susani shine motoci sunada categories masu yawa amma wadanda sukafi zama popular a duniya sune kamar haka
1. SEDAN
2. SUV
3. VAN
4. PICK UP TRUCK
Kuma ko wane daya daga cikin wadannan hudun yanada tarin bayani me zaman kansa.

wannan shine taqaitaccen bayanina akan wadannan motocin, kuma a inda nike ina taimaka ma mutane da bayanai masu dauke da hujjoji masu gamsara akan motarda tafi dacewa su saya domin gudanarda abubuwansu da yau da kullun.

Inada YouTube channel amma ban fara yin komai ba akai kuma ina buqatar shawarwari akai daga gareku akan yadda za inganta page dina da yadda zan fara aiki da YouTube channel dina domin yin video review akan kowace mota dana samu dama akai. Fatan alkhairi gareku.

01/05/2026

Shugaban matasan jam'iyyar adawa ta ADC ɓangaren Nafiu Bala Gombe, Hon. Sultan Ahmed Bello ya sanar da ajiye muƙaminsa.

A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, Hon. Sultan ya ce ya ɗauki matakin ne saboda yadda yake fuskantar barazana da kuma shan tsinuwa da munanan addu'o'i daga wajen al'umma saboda abin da ya ke faruwa da kuma goyon bayan Nafiu Bala da ya ke yi.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da kotun ƙolin Najeriya ta tabbatar da shugabancin jam'iyyar ADC ɓangaren Sanata David Mark....

Kun yafe masa?

06/09/2025

Walkahi shi ke fadi ni kejin kunya. Ya rabbi kada ka jarrabeni na lalace kamar wannan

HG Autoreviews 04/01/2024

Car reviews is what we do. If you want to buy any type of cars from any brand in the world we will always help you with detail information for you to decide the best car for you to to buy

HG Autoreviews We open this page to share our knowledge on vehicles. We review any type of cars from any car brands

Photos 06/06/2014

Koba2005

Photos 06/06/2014

Kanta

Want your business to be the top-listed Autos & Automotive Service in Argungu?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Website

Address

Along Farin Tanki Argungu
Argungu

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when HG Autoreviews posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Subscribe

We will notify you when anything happens in Argungu.