Pantamiyya Reporters

Pantamiyya Reporters

Share

PANTAMIYYA REPORTERS

PANTAMIYYA AMANA

Photos from Pantamiyya Reporters's post 03/10/2026

Yusuf Bello coordinator Pantami youth and media na Tabra/Liji ya buga billboards guda 35 a aljihunsa domin tallata jagora Professor Isa Ali Pantami inda zai rabawa wakilansa domin a ciki gaba da tallata Malam

03/10/2026

Bari Mu Kara Jaddada Aqidar Mu

Pantamiyya! ✊🏼✊🏼

02/10/2026

Thanks for being a top engager and making it on to my weekly engagement list! 🎉 Umar Abdulmumin Saha, Sadiq Baban Zainab, Ibrahim Jibril Biu, Abdulrasheed Mohammed, Musa Dahiru, Itz Abbancy, Kabeer Usman Aljabbary, Sadiq Salihu, Dauda Buba Dauda, Uzairu Musa, Imrana Abdullahi, Bashir Shuaibu Umar, Moussa Maman Mansour, Ahmed Garba, Muhammad Ashiru Malgwi, Sani Magaji, Hajji Ali, Muhammad Hamza, Hayatu Umar Lwan, Musa Jano Jumbam, Baban Adinan Bello, Aliyu Haidar

29/09/2026

Professor Isa Ali Pantami Ya Zama Halastaccen Dan Takarar Gwamnan Jihar Gombe Karkashin Jam’iyyar PDP

Professor Isa Ali Ibrahim Pantami ya lashe sabon zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP na takarar Gwamnan jihar Gombe a zaben 2027.

An gudanar da zaben ne a yau, Talata 29 ga Satumba, 2026, inda Professor Isa Ali Pantami ya samu nasarar zama dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar Gombe.

Professor Isa Ali Pantami ya samu kuri'u dubu 2,054.

Khamisu Mailantarki yazo na biyu da kuri'u 389.

Usman Garry yazo na uku da adadin kuri'u 112.

Adadin membobin jam'iyyar PDP da s**a yi zaben fidda gwani a fadin jihar Gombe 2,555.

29/09/2026

Masoya Malam Muna Cikin Alkhairi, Muce Alhamdulillahi

Photos from Pantamiyya Reporters's post 29/09/2026

Yanzu haka ana gudanar zaben fidda gwani a gundumar Doho, karamar hukumar Kwami.

Photos from Pantamiyya Reporters's post 29/09/2026

Yanzu haka ana gudanar da zaben fidda gwani a gundumar Kushi karamar hukumar Shongom.

28/09/2026

Gombe Ta Malam ce In Sha Allah 🤲✅🤸

28/09/2026

DA DUMI-DUMI: Gwamnatin Jihar Gombe Ta Dauki Nauyin Matasa Tare Da Musu Ragistar Katin PDP Domin Su Tada Fitina A Zaben Fidda Gwani Na PDP A Gobe Talata
...Iya list din membobin PDP da hukumar INEC ta kawo bisa tanadin dokar zabe, su ne za su iya shiga zaben fidda gwani na gobe Talata.

Jam’iyyar PDP reshen Jihar Gombe ta ce ta samu bayanai daga wasu majiyoyi da ta bayyana a matsayin amintattu, cewa gwamnatin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ta ɗauki wasu mutane domin ƙera katunan zama ɗan jam’iyyar PDP na bogi guda dubu ashirin (20,000).

A cewar sanarwar, ana zargin an shirya waɗannan katuna ne domin amfani da su a sabon zaɓen fidda gwani na ɗan takarar gwamnan PDP, wanda za a gudanar ranar Talata, 29 ga Satumba, 2026, bisa umarnin Babbar Kotun Tarayya da ke Gombe.

PDP ta kuma yi zargin cewa za a rarraba waɗannan katunan bogi guda 20,000 ga mata da wasu mutane, tare da ba kowane mutum kusan Naira 10,000 domin jan hankalinsa.

Jam’iyyar ta ƙara da zargin cewa manufar ita ce a tayar da rikici yayin zaɓen, sannan a ɗora alhakin rikicin kan PDP. Ta ce APC na son yin amfani da hakan a matsayin hujjar cewa an samu rikici a zaɓen fidda gwanin tare da hana wasu mutane kaɗa ƙuri’a, alhali PDP ta ce mutanen ba mambobinta ba ne kuma an ba su katunan bogi ne.

PDP ta ce waɗanda kawai s**a yi rajista da jam’iyyar kuma aka miƙa sunayensu ga Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), bisa tanadin dokar zaɓe, su ne za su iya shiga zaɓen. Jam’iyyar ta ce tana da hujjojin da ke tabbatar da hakan.

Sanarwar ta kuma soki gwamnatin Gwamna Inuwa Yahaya, tana mai zargin cewa tana amfani da dukiyar jihar wajen ɗaukar masu amfani da TikTok daga wasu jihohi domin su tallafa mata wajen ɓoye gazawarta daga idon jama’a. PDP ta ce al’ummar Gombe suna jiran lokacin zaɓe domin yanke hukuncinsu ta hanyar ƙuri’a.

A ƙarshe, PDP ta buƙaci mambobinta su kasance masu zaman lafiya tare da bin doka yayin gudanar da zaɓen. Haka kuma ta yi kira ga hukumomin tsaro da su binciki zarge-zargen domin gano gaskiya tare da ɗaukar matakin da ya dace.

Sanarwar ta ƙare da cewa:

“Tsoron PDP a Jihar Gombe shi ne farkon hikima.”

Abdulkadir Ahmad Dukku
Sakataren Yaɗa Labarai na PDP, Jihar Gombe.

28/09/2026

Professor Isa Ali Pantami, CON, PhD (Wazirin Pantami), ya kasance ɗan siyasa na farko a Jihar Gombe wanda al’umma s**a dade suna jiran ya bayyana aniyarsa ta yin takarar Gwamnan Jihar.

Cikin ƙanƙanin lokaci, hankalin al’umma ya karkata zuwa gare shi, saboda tarihin shugabancinsa, nagartarsa, gaskiyarsa, riƙon amana, da kuma irin sadaukarwar da ya yi wa ƙasar Najeriya.

Hakan ne ya sa babu buƙatar ci gaba da gabatar da wanene Pantami, Gombawa mun san shi.

Shi ne tsohon Darakta-Janar na NITDA, wanda ba mu taɓa samun irinsa ba.

Haka zalika, shi ne tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arziƙin Zamani na Najeriya, wanda Jihar Gombe ba ta taɓa tura wani ɗa da ya zama abin alfahari ga jihar kamar sa ba.

Shi ya sa muka ce:

GOMBE TA MALAM CE 2027, IN SHA ALLAH.

SAMBO ✍️
28/09/2026

Want your business to be the top-listed Media Company in Gombe?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Website

Address

Gombe

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Pantamiyya Reporters posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Subscribe

We will notify you when anything happens in Gombe.