Possible Update
Shafin sahihan labarai, siyasa, harkokin gwamnati da al’amuran yau da kullum a Kano da Najeriya. Domin Karin bayani 07010552096
Ku biyo mu domin samun sahihan bayanai cikin gaggawa. “Muryar Gaskiya da Cigaba”.
27/08/2026
Zabi gwanin ka👌🏻🫵🏼
19/08/2026
Hukumar Tsaro ta farin kaya ta K**a Wani Jami'inta (DSS) Na Bogi A Abuja.
Jami'in bogin mai suna Moferewa Maiye, yanzu haka yana tsare a komar hukumar dake Abuja domin cigaba da bincikarsa.
Me zaku ce?
19/08/2026
Yar Najeriya Tazo Ta Daya A Musabaƙar Alƙur’ani Ta Duniya Bangaren Tafsiri
Maryam Ibrahim Dan’azumi daga Jihar Gombe ta zo ta ɗaya a sashen Tafsiri na mata a gasar Musabaƙar Alƙur’ani ta Duniya karo na 46 da ake gudanarwa a Masarautar Saudiyya.
Wannan babbar nasara ce ba ga Maryam kaɗai ba, har ma da Jihar Gombe da Najeriya baki ɗaya.
Maryam tana cikin ƴan Najeriya huɗu da s**a wakilci ƙasar a wannan gagarumar musabaƙa, tare da Hafsa Muhammad Sada daga Jihar Kano, Abdullahi Asil daga Zamfara da Abdulmalik Muhammad Inuwa daga Taraba.
Muna taya Malama Maryam Ibrahim Dan’azumi murna bisa wannan gagarumar nasara. Allah Ya ƙara mata ilimi, basira da ɗaukaka, Ya sanya Alƙur’ani yazamo hujja a gare ta ba akanta ba.
kuma Ya ƙara ɗaukaka Najeriya da yayanta a fadin duniya bakidaya.
Amin.
18/08/2026
Alhamdu lillah!
Rahoton DW Hausa ya ce kafafen yaɗa labarai na Turkiya sun ce tsohon ɗan wasan na Real Madrid ɗin mai shekaru 53 ya karbi shahadar ne kimanin makonni huɗu da s**a gabata, yayin wata ziyara da ya kai wurin Sheikh Jihad Hamada, wanda ke cikin fitattun malaman ƙungiyar Musulmi a Brazil.
Sai dai har yanzu Roberto Carlos bai fitar da wata sanarwa kai tsaye da ke tabbatar da musuluntar sa ba, don haka rahoton na ci gaba da kasancewa zargi da ke buƙatar tabbatarwa daga bakin ɗan wasan da kansa.
18/08/2026
TAWAGAR SSR/SR TAYI TARO NA MUSAMMAN DOMIN ƘARA WAYAR DA KAN JAMA’A GAME DA NASARORIN GWAMNATIN JIHAR KANO
A Yammacin Jiya Litinin, 17 ga Agusta, 2026
Shugabancin SSR/SR Forum na Jihar Kano ya gudanar da wani taro na musamman domin tsara hanyoyin da za su ƙara inganta ayyukan dandalin wajen wayar da kan jama’a game da nasarori da shirye-shiryen Gwamnatin Jihar Kano.
A yayin taron, shugabannin dandalin sun tattauna muhimman dabarun ƙarfafa haɗin kai da haɗin gwiwa tsakanin mambobi, tare da samar da ingantattun hanyoyin isar da sahihan bayanai game da ayyukan raya ƙasa da shirye-shiryen da Gwamnatin Jihar Kano ke aiwatarwa.
Dandalin ya bayyana aniyarsa ta ci gaba da amfani da kafafen sadarwa da sauran hanyoyin da s**a dace wajen wayar da kan al’umma da bayyana ayyukan ci gaba da gwamnatin Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ke aiwatarwa domin amfanin al’ummar jihar.
Haka kuma, shugabannin sun jaddada cewa za su ci gaba da gudanar da ayyukansu cikin tsari, haɗin kai, jajircewa da sadaukarwa, tare da ƙarfafa mambobi wajen isar da saƙon ci gaba ga jama’a cikin ingantaccen tsari.
Taron ya kuma mayar da hankali kan shirye-shiryen da s**a shafi kamfen ɗin sake zaɓen Gwamna Abba Kabir Yusuf, inda aka tattauna hanyoyin ci gaba da wayar da kan jama’a da bayyana nasarorin da gwamnatin ta samu.
JAM’IYYAR OBI DA KWANKWASO KURI’U NAWA S**A SAMU A OSUN?
Da zikirin Allah kadai zukata ke samun nutsuwa🥰👌
Click here to claim your Sponsored Listing.