Taska

Taska

Share

Dubban Hanyoyi na Dabarun saukake Fahimtar rayuwa.

27/09/2026

Mene ne gaskiyar wannan lamari 🫣😅🤔🤔

22/09/2026

Kamar dai yadda aka saba a kowace shekara, ahamdulillah wannan karon ma mun sami yara masu hazaƙa sosai, kuma a yau ɗin nan ne muka ɗaura su akan hanyarsu na zuwa ƙasar ketare (Turkiya) don samun ƙarin ilimi har izuwa matakin da za su iy.

Ɗaya, ya ce min yana so ya zama injiniyar wutar lantarki, ɗayan kuma ya ce yana so y zama babban malami mai koyarwa……

Wani sirri da na fahmta shine:
Wallahi duk shekara idan muka sami yara masu ƙoƙari da hazaƙa haka, za ka samu iyayensu mata ne suke tsaya musu dare da rana har sai sun zama wasu….

Wallahi yau ɗin nan maman ɗaya daga cikinsu, tun safe take ofis dinmu har magriba, tana tare da yaron nata, har sai da shiga wurin hawa jirgi ya rabasu….

Photos from Taska's post 22/09/2026

Me ya sa idan ka ji ba ka da lafiya ta fuskar mafitsara ko kasa gamsar da iyali, kai koma mene ne da ya shafi mara, wanda ya kamata ka fara nema shine likita ba wai masu maganin gargajiya ba?.

Saboda likita shine bakaniken jikin danadam, shine wanda zai haska, ya auna kana ya bada maganin ko shawarar da ta dace.

Dukka masu maganin gargajiya lalube suke yi a duhu, ba su san komai ba, shi ya sa za ka samu suna cewa: a dogara da Allah, a sha maganinsu.

Abin da ya kamata mu sani shine: wallahi magungunan gargajiya sun fi cutar da mutane sama da yadda za su amfanesu.

Abin takaici:
Kana shiga kasuwa, za a cika maka kunne da kalaman batsa cikin lasofikoki!
Kana dawuwa gida ka kunna tv ko radio don ka huta za a cika maka kunne da tallace tallacen maganin ƙarin ƙarfi!!!

Wallahi duk abin da ya sauka daga kan Naturality nasa to sai ya cutar!!!!!

19/09/2026

Zan baku gajeren labari mai ban mamaki!

Wannan mutumi da kuke gani, ya biyo tawagar masu bada tallafi ne a nan yankin Afrika a matsayin volunteer (mai aikin sa kai).

To a ƙungiyarmu muna da ɗaukan nauyin marayu - Haka yana nufin za mu riƙa tura wa maraya kuɗi a duk watan duniya har sai ya girma.

To wannan bawan Allah yana ɗaukan nauyin wata marainiya tun kimanin shekaru 3 da s**a wuce, ta yadda ya sadaaukar da wani ƙisimi na albashinsa yake tura wa wata marainiya da bai taɓa haɗuwa da ita ba.

To da s**a zo ziyara; tun da mu mun san waɗanda ke ɗaukan nauyin kowane maraya, sai muka shirya masa Surprise.

Sai muka sayi wasu kayayyaki na kyaututtuka muka shiga gidan watannan marainiya da kuke gani. Bayan mun gama gaisawa sai muka nuna masa ID card dinta muka tambayarshi ko ya ganeta? Cikin dariyar wasa ya ce; banda abinku a ina za taɓa saninta!?

Sai muka ce masa to "ka duba email link dinka za ka bayanai game da ita da kuma wannan unguarded da muka zo" wato ita ce wanda kake tura wa kuɗi da kimarsa ya kusa dubu dari na naira a kowane wata!

Sai ya zabura ya miƙe, kuma ya tsaya nesa da ita kaɗan.
Sai idanunsa s**a cika da ƙwalla.

Ina tabbatar muku bai sake iya cewa komai ba sai abin da ba a rasa ba, har sai da muka yi musu sallama muka bar gidan.

Abin mamaki a ƙissar shine: Bayan mun dawo mun sami wuri muna zauna, abin da ya faɗa shine: mun ɓata masa tsari amma ba komai ya yafe mana!?

Ashe tsarin da ya yi shine: zai ɗauki nauyin marayu a iya ƙarfinsa, kuma har abada ba ya so su san shi ko shi ya san su.

Photos from Taska's post 13/09/2026

Mutane da yawa suna tambaya cewa idan aka ɗura wa mace ciki: (ina uwar hanji da su tumbi suke zuwa?)

A hakika shine: ciki yana farawa ne daga ƙasan tumbi; kuma mafi yawanci tun ciki yana sati 3-6 yake fara zama ɗan ƙullutu ƙarami da kusan halittu nasa na mutum suke fara bayyana.

Daga nan kuma zuwa wata biyar already ya zama cikakkem mutum da zai ci gaba da girma.

To duk lokacin ciki ya ƙara girma yaron yana hankaɗa kayan cikin ne su koma gefe wasu kuma su yi sama, ciki kuma dama kamar roba yake, haka zai yi ta buɗewa sannu a hankali; amma da zaran ta haihu; a hankali a hankali Kayan ciki za su dawo wurinsu, ciki kuma shi ma mafi yawa yana dawuwa yadda yake ne.
Idan bai dawo ba, ko ya yi layi-layi to shi ma akwai dabarun da ake masa a gargajiyanci da ma a likitance.

Amma akwai wasu manyan kuskurori har guda uku da mata da yawa suke yi ba tare da sun sani ba.
👇🏾👇🏾👇🏾

12/09/2026

Digon ruwa mafi tsada a duniyan nan shine ruwan ƙarin kunama, da kuɗin galan ɗaya ya kai kimanin Naira biliyan hamsin. 50b N

Ina ba wa matasa shawara da su koyi yadda ake tatse wannan ruwan, domin ko kopi ɗaya ka samu ka tara wallahi ka yi arziki….. - kuma ba abu ne mai wuya sosai ba-.

Ana yin magunguna da yawa da shi, da ya haɗa da maganin cancer (ciwon daji) da cire raɗaɗi da warkar da infection din da ya ƙi jin magani, d.s.

Mata za su fi iya tarawa sannu a hankali sakamakon sun fi zama wuri ɗaya, za su iya kiwata ita kanta kunamar kuma lokaci bayan lokaci su riƙa tatsa suna tarawa har su cika jarka ma in suna so - kawai dai yana buƙatar hakuri ne -

09/09/2026

Wannan shine shararren mai kuɗin nan Marigayi Malam Tiny.
Wanda Allah ya yi masa Wafati a sailin da ake yi masa aiki na ƙara girman mafitsara a ƙasar Tailanda.

Bayanai suna nuna a binnesa cikin makara na zinare da kimar kudinta ya kusa biliyan daya na Naira.

04/09/2026

Ina da haƙƙin yin wannan tambayan !

Tun muna yara ake yi mana alluran riga kafi, da an haifi mutum a asibiti za su zo yi masa, kuma wurin har ya yi tabon da ba ya ɓacewa komin tsufa!

To ita wannan rigakafin mene ne ake kafewa kuma mene tasirint, sannan mene bambanci tsakanin wanda aka yi masa da wanda ba a yi masa ba??

Shin ina da haƙƙin na hana a yi wa yarona?!!!

Wanda bai sani ba ya yi mana tagging din likitoci!

01/09/2026

Kwata-kwata shekara 10 kenan da yin wannan hoton, lokacin ina jami’a amma yanzu in na nuna muku watannan yarinyar sai kun razana.

Abin da yake ɗauremin kai shine:

Wai tsakanin maza da mata wa s**a fi saurin girma ne 🤔

Saboda akwai ƙannena maza da na taba yin wani tafiya na yi kimamin shekara 8 ban dawo ba, Da na zo na gansu sai da na ji gabana ya faɗi, dukkansu sun kai bishiya girma.

Kuma ni ma akwai matan da s**a girmeni yanzu na fi su girma 😅

30/08/2026

Wannan shine abin da ya kamata kowace mai ciki ta riƙa yi kullum da daddare ko da rana tare taimakon mijinta da zai riƙa biyowa ta baya yana danna ƙashin bayanta yana mata tausa har ta sami gamsuwa ta yadda za ta iya yin bacci mai dadi.

Wannan yanayi yana hana samun yawan ciwon baya ga masu ciki.
Kuma yana taimakon abin cikin nata ya riƙa samun excercise a kodayaushe!!!

Allah ya taimaka.
Allah ya raba lafiya.

Want your practice to be the top-listed Law Practice in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Website

Address

Kano
810241

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Taska posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Subscribe

We will notify you when anything happens in Kano.