TajTech
We empower people with modern digital skills needed for today’s world.
At TAJTECH, we provide professional computer training, internet services, and tech education to help students, graduates, and entrepreneurs succeed.
Barka da jumaa TajTech
24/06/2026
Kun lura cewa wani lokacin idan ka sanya wayarka a chaji tana dade wa ba ta cika ba, ko kuma tana yin zafi sosai?
Ga sirrika guda biyu da zasu baka mamaki kuma zasu taimaki rayuwar wayarka:
Cire Cover (Case) Din Waya Lokacin Chaji: Yawancin cover na roba ko na fata suna rike zafi ne. Idan waya tana chaji tana yin dumi, idan akwai cover zafin ba zai fita ba, wannan yana rage gudu da ingancin chajin. Cire cover din ka gani, zata yi chaji da sauri!
Kada Ka Rinka Yin Chaji Da Laptop Ko TV: Sanya USB a jikin Laptop ko Talabijin domin yin chaji yana rage rayuwar batir saboda karfin wutar (Voltage) da ke fitowa daga jikinsu bai kai daidai yadda aka tsara wayarka ta karba ba. Yi amfani da ainihin chajarka ta jikin bango (Wall Socket).
Shawara Ta Musamman: Idan chajarka ta asali (Original) ta lalace, kada ka sayi chajar jami'a ta ₦500. Tana kona board din waya! Gara ka zabi mai kyau mai dauke da garanti.
24/06/2026
📱 Kuskuren da Yawancin Masu Waya Suke Yi Kullum
⚠️ Ka san cewa cika memory na waya gaba ɗaya na iya sa wayarka ta fara yin nauyi da saurin ɗaukar zafi?
Abin da ya kamata ka yi:
✅ Ka bar aƙalla 10% - 20% na storage a buɗe.
✅ Ka goge apps da ba ka amfani da su. ✅ Ka share videos da files marasa amfani.
23/06/2026
Kafin ka sayi UK Used Phone, ka duba abubuwa 3:
✅ Battery Health
✅ Network Unlock
✅ Original Screen
Mutane da yawa suna rasa kuɗinsu saboda ba su duba waɗannan abubuwa ba.
23/06/2026
"Yadda Zaka Hana Wayarka Dinke Memory (Space) Ba Tare da Ka Goge Hotunanka Ba 📂"
Sau da yawa zaka ga wayarka tana kawowa "Storage Space Running Out" alhalin baka sanya sabbin abubuwa ba. Ga inda matsalar take:
Shiga Settings > Apps > Manage Apps.
Zabi apps din da ka fi amfani dasu kamar Facebook, TikTok, ko WhatsApp.
Sai ka danna "Clear Cache" (Kada ka danna Clear Data domin kar ya goge maka komai).
Wannan "Cache" din wasu kura ne da kashin data da apps din ke tarawa, share su zai ba wayarka sarari sosai kuma zata daina nauyi.
Jada kaje ka gwada yanzu, sannan ka dawo ka fada mana ko ka samu space
23/06/2026
📱 Samsung Galaxy A54 vs iPhone 12 🔥
Idan kana da kuɗin siyan waya ɗaya kawai, wacce za ka zaɓa? 🤔
Samsung Galaxy A54
✅ 120Hz Super AMOLED Display ✅ 5000mAh Battery mai ɗorewa ✅ Android mai sauƙin amfani ✅ Sabbin software updates ✅ Ƙarin damar amfani da memory card
iPhone 12
✅ Ƙarfin A14 Bionic Processor ✅ Kyakkyawar Camera musamman video ✅ Premium Design ✅ iOS mai sauri da tsaro ✅ Dogon lokaci na software support
Kai fa?
🔵 Samsung Galaxy A54 🍎 iPhone 12
Rubuta "A54" ko "iPhone 12" a comment sannan ka faɗi dalilinka. 👇
Ni kuma zan ce:
Idan kana son batiri mai ɗorewa da Android 👉 A54
Idan kana son camera da performance 👉 iPhone 12
05/06/2026
Ko daina sawa kanku pressure idan kunzu Bude icloud yaki Hawa, wannan ba issues bane
Indai waya nml ka take to tana Bude icloud
Idan kaga ga gwada Bai budeba to daga server din chan apple dinne
Mutun zai sai waya sai yayi ta chema ya kasa Bude icloud Wani har ya fara tunanin ko ka bada waya mara kyau ne
Ba haka bane badaga waya bane daga kansu apple dinne
Nayi rubutu kan yadda ake Bude icloud chikin sauki idan ka karanta post din Kuma still kana Shan wahala wajen Bude icloud baza na Dan karama wasu hinges din dazasu tai maka
Duk lukachin da kakesun ka Bude icloud ka bari sai chikin dare ko wajen asuba haka
A Wannan lukachin anfi samun network Mai kyau sai kuma ka samu waya Mai karfin network ka kayi connecting na WiFi
Sai Abu na gaba Shine Gmail da Kai anfani dashi wajen Bude icloud yazama accessible
Idan ka gwada Bude icloud sai bayiwuba to karkai ta gwadawa
Dakayi sau daya sau biyu sai kabari zuwa Wani lukachi chan haka sai ka Kara gwadawa
To inshallah idan Kai haka Zaka bude icloud naka chikin sauki batare ma da Wani ya saniba
Allah yasa mudache 🤝
TajTech
Mai waya
07068936900
Kano Nigeria
04/06/2026
Akan wannan wayar Iphone s**a fara saka wani feature Mai matukar anfani musanman ga yen' birni masu capacity, wannan feature ita ake Kira da cinematic
Bakowa bane zai baka labarin yadda take futar da yen gayu kunya ba sai Wanda yake anfani da ita sosai
IPhone 13 tanadaga chikin Iphone masu rikon charging da Kuma kyan design 👌
Idan kanasun Iphone 13 original non display direct UK Mai capacity zan baka ita a
355k daga yau zuwa gobe nml price nata 375k ne
So come and buy before you hear sold
TajTech gadgets
07068936900
Kano Nigeria
Click here to claim your Sponsored Listing.