Darma Tv

Darma Tv

Share

Muna kawo labaran abubuwan da suke faruwa labaran siyasa dama nishadantarwa

04/09/2026

🔴 DARMA TV – KAI TSAYE

GOBARA TA TASHI A KASUWAR KOFAR WAMBAI A KANO

Wata gobara ta tashi a daren nan a Kasuwar Kofar Wambai, da ke cikin birnin Kano, musamman a yankin da aka fi sani da ‘Yan Robobi.

Rahotannin farko daga wajen kasuwar sun ce gobarar ta tashi ne a yankin ‘Yan Robobi, inda ake gudanar da harkokin kasuwanci da dama.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, ba a samu cikakken bayani kan musabbabin tashin gobarar ko yawan barnar da ta haddasa ba.

Ana sa ran jami’an Hukumar Kashe Gobara da sauran jami’an ceto za su isa wurin domin dakile yaduwar wutar.

Kasuwar Kofar Wambai na daga cikin manyan kasuwannin Kano, kuma tana da sassa daban-daban na kayan kasuwanci, ciki har da robobi.

DARMA TV za ta ci gaba da bibiyar lamarin, kuma za mu kawo muku karin bayani da zarar hukumomi sun tabbatar da halin da ake ciki.

DARMA TV — KAI TSAYE | LABARI DAGA KANO

02/09/2026

🔴 DARMA TV –

GWAMNA ABBA YA YI ALLAH-WADAI DA HARE-HAREN ’YAN BINDIGA A KANANAN HUKUMOMI HUDU NA KANO

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya yi Allah-wadai da hare-haren ’yan bindiga da s**a afku a wasu sassan Kananan Hukumomin Garun Mallam, Rogo, Bebeji da Gwarzo.

A cikin wata sanarwa da Kakakin Gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, Gwamna Abba ya bayyana hare-haren a matsayin abin takaici da tayar da hankali, tare da mika ta’aziyya ga iyalan wadanda s**a rasa rayukansu.

Gwamnan ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar na aiki tare da hukumomin tsaro domin daukar matakan gaggawa, da karfafa tattara bayanan sirri, sa ido da kuma inganta tsaro a yankunan da abin ya shafa.

Haka kuma, ya bukaci al’umma su ci gaba da bai wa jami’an tsaro hadin kai ta hanyar bayar da sahihan bayanai domin dakile masu aikata laifuka.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sake jaddada kudirin gwamnatinsa na tabbatar da zaman lafiya da kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar Kano.

DARMA TV – KAI TSAYE.

Photos from Darma Tv's post 25/08/2026

DARMA TV – KAI TSAYE

YANZU-YANZU: AN K**A MOTAR DA AKE ZARGIN ƊAUKE DA MIYAGUN KWAYOYI A BAJALLABE

KANO: Kwamitin Ƙar-Ta-Kwana mai yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi, ƙarƙashin jagorancin Barrister Muhyi Magaji Rimin Gado, ya samu nasarar dakile wata mota da ake zargin tana ɗauke da miyagun ƙwayoyi, yayin da ake ƙoƙarin shigar da su cikin al’umma a unguwar Bajallabe da ke Kano.

Rahotanni sun bayyana cewa tun da farko, ’yan kwamitin unguwar Bajallabe ne s**a lura da motar, inda daga bisani s**a sanar da kwamitin Ƙar-Ta-Kwana.

Bayan samun bayanin, jami’an kwamitin ƙarƙashin jagorancin CSP Bashir Gwadabe, O/C Anti-Daba, s**a yi wa yankin tsinke, lamarin da ya kai ga dakile motar.

A halin yanzu, an kai motar ofishin cajin Rijiyar Zaki, domin ci gaba da bincike, tattara bayanai da kuma ɗaukar matakin da ya dace bisa doka.

Barrister Muhyi Magaji Rimin Gado ya yaba wa ’yan kwamitin unguwar Bajallabe bisa jajircewa da kuma yadda s**a gudanar da aikin cikin nutsuwa, wanda ya taimaka wajen samun wannan nasara.

Kwamitin Ƙar-Ta-Kwana ya sake yin kira ga al’umma da su ci gaba da sanya ido a yankunansu, tare da gaggauta sanar da hukumomi ko kwamitin kan duk wani motsi da ake zargi ko wanda bai yi musu daidai ba.

DARMA TV – KAI TSAYE
Rahoto mai tushe daga cikin al’umma.

@

22/08/2026

DARMA TV – KAI TSAYE

FAGGE: ‘YAN MAJALISUN TARAƊI SUN TALLAFA WA ‘YAN GWAGWARMAYA

FAGGE, KANO: ‘Yan majalisun tarayya masu wakiltar al’ummar Ƙaramar Hukumar Fagge, sun gudanar da wani shiri na tallafawa ‘yan gwagwarmaya da kayan dogaro da kai.

A yayin shirin, Hon. Tukur Muhammad da Hon. Barr. Muhammad Bello Shehu sun tallafa wa masu cin gajiyar shirin da kayayyakin empowerment da s**a haɗa da babura, kekuna, injuna da kuma tallafin kuɗi, domin ƙarfafa musu gwiwa wajen gudanar da sana’o’i da neman abin dogaro da kai.

Masu ruwa da tsaki sun bayyana cewa irin wannan tallafi na taimakawa wajen rage zaman kashe wando, tare da bai wa matasa damar dogaro da kansu.

Rahoton DARMA TV ya tabbatar da cewa shirin ya samu karɓuwa daga mahalarta, yayin da ake kallon matakin a matsayin wata hanya ta ƙarfafa al’umma da bunƙasa tattalin arziƙin jama’a.

DARMA TV – KAI TSAYE
Rahoto daga Fagge, Kano.

21/08/2026

DARMA TV – KAI TSAYE

DA DUMI-DUMI: JIGO A APC KANO, ALHAJI HAMZA USMAN DARMA YA RASU

KANO: Allah Ya yi wa wani fitaccen jigo a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a Kano, Alhaji Hamza Usman Darma, rasuwa.

Rahotanni sun tabbatar da cewa Alhaji Hamza Usman Darma ya rasu a yau, Juma’a, inda rasuwarsa ta jefa iyalansa, ’yan uwa, abokan arziki da ’yan jam’iyyar APC cikin alhini da jimami.

Marigayin ya kasance cikin mutanen da s**a taka muhimmiyar rawa a harkokin siyasa da ayyukan jam’iyya a Kano.

A yayin da ake bayyana alhini bisa wannan babban rashi, ana addu’ar Allah Ya jikansa da rahama, Ya gafarta masa kurakuransa, Ya sanya Aljannatul Firdausi ta zama makomarsa.

Haka kuma, ana roƙon Allah Ya bai wa iyalansa, ’yan uwa da abokan arziki haƙurin jure wannan babban rashi.

DARMA TV – KAI TSAYE

Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un.

Photos from Darma Tv's post 20/08/2026

DARMA TV – KAI TSAYE

INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI’UN: TSOHON KANSILAN FAGGE, HON. BALA ISA LORE, YA RASU

FAGGE, KANO: Allah Ya yi wa tsohon Kansilan Fagge, Hon. Bala Isa Lore, rasuwa a ƙasar Masar (Egypt), bayan doguwar jinya da ya sha fama da ita.

Hon. Bala Isa Lore ya kasance tsohon Kansila a Mazabar Fagge C, inda ya taka rawa wajen wakiltar al’ummar yankin.

Marigayin ya rasu ne bayan doguwar jinya, lamarin da ya jefa iyalai, ‘yan uwa da abokan arziki cikin alhini da jimami.

A wannan lokaci na babban rashi, ana roƙon Allah Madaukakin Sarki Ya gafarta masa kurakuransa, Ya jikansa da rahama, Ya sanya Aljannatul Firdausi ce makomarsa.

Haka kuma, ana addu’ar Allah Ya ba iyalansa, ‘yan uwa da daukacin al’ummar Fagge haƙurin jure wannan babban rashi.

Daga DARMA TV – KAI TSAYE

Allah Ya jikansa da rahama. Amin.

19/08/2026
18/08/2026

daga shafin Real Madrid on Instagram 😂⚪️ — suna kamar za a fara ganin abubuwa masu ban dariya! Hala Madrid! 🤍😂⚽️

Photos from Darma Tv's post 17/08/2026

DARMA TV – KAI TSAYE

APC MEDIA FORUM FAGGE TA ZIYARCI HON. MUHAMMAD BELLO SHEHU

KANO — 17 GA AGUSTA 2026: Ƙungiyar APC Media Forum, Fagge Chapter, ƙarƙashin jagorancin Dr. Adamu Danjuma Isah Bakin Wapa, ta kai ziyarar girmamawa ga ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Fagge, Hon. Barr. Muhammad Bello Shehu.

Ziyarar ta kasance domin nuna goyon baya da ƙara ƙarfafa haɗin kai tsakanin ƙungiyar da ɗan majalisar, tare da jaddada cikakken goyon bayansu ga tsarin Jam’iyyar APC, tun daga matakin ƙasa da jiha har zuwa Fagge.

A yayin ziyarar, ƙungiyar ta kuma bayyana aniyarta ta ci gaba da bayar da gudunmawa wajen ƙarfafa jam’iyyar da haɗin kan ‘ya’yanta.

A ƙarshe, shugabannin ƙungiyar sun yi addu’a ga shugaban ƙasa da sauran shugabannin jam’iyyar, inda s**a roƙi Allah Ya ba su ikon sauke nauyin da ke kansu cikin sauƙi da nasara.

DARMA TV — KAI TSAYE!

@

Photos from Darma Tv's post 17/08/2026

KWANKWASO YA HALARCI TARON MAULUDI A YAKASAI

KANO: Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma jagoran siyasar Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya halarci taron Mauludin shekara-shekara da Sani Kwangila Yakasai ya shirya.

Taron, wanda ya gudana a Yakasai, ya samu halartar al’umma da dama, inda aka gudanar da addu’o’i da kuma wa’azi kan rayuwar Manzon Allah ﷺ da koyarwarsa.

Kasancewar Kwankwaso a wajen taron ta ƙara wa taron armashi, yayin da mahalarta s**a nuna farin ciki da yadda aka gudanar da wannan muhimmiyar ibada.

DARMA TV – KAI TSAYE

@

Want your public figure to be the top-listed Public Figure in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Telephone

Website

Address

Kano
70010

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Darma Tv posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Subscribe

We will notify you when anything happens in Kano.