Hausa Digital RTV

Hausa Digital RTV

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Hausa Digital RTV, News & Media Website, Katsina.

Hausa Digital Radio and Television, shafin labarai ne mai zaman kan shi daga jihar Katsina, kuma yana daukar labarai daga dukkan jihohin Najeriya da sauran kasashen ketare

13/09/2026

Jam'iyyar ADC Ta Yi Babban Rashi A Matakin Kasa....

Mataimakin Sakatare na jam'iyyar adawa ta ADC a matakin kasa Alhaji Hassan Muhammadu, ya ajiye mukamin shi tare da ayyana ficewa daga jam'iyyar.

Ficewar tashi daga ADC tana cikin wani sakon murabus ɗin da ya aike ne zuwa ga Shugaban ADC na Unguwar Bojude, a Ƙaramar Hukumar Kwami ta Jihar Gombe.

Hassan Muhammadu, wanda shi ne Mataimakin Sakatare ADC na Ƙasa, kuma Sakataren Kwamitin aiki na yankin Arewa maso Gabas, ya ce ya yanke shawarar ficewa daga jam’iyyar ne bayan zurfafa tunani.

A cikin wasiƙar, ya ce, “Bayan zurfin tunani, ina son sanar da ficewata tare da jama’ata daga ADC, sannan na sanar da murabus daga mukamina na Mataimakin Sakataren Ƙasa da kuma Sakataren Yankin Kwamitin Aiki na Yankin Arewa maso Gabas na jam’iyyar.”

Hassan Muhammadu ya kuma nuna godiyarsa ga jam’iyyar da shugabanninta bisa damar da s**a ba shi ya yi aiki a matakin ƙasa.

Ya bayyana cewa, an aika kwafin wasiƙar murabus ɗin nasa zuwa ga Shugaban Ƙasa na ADC, Sanata David Mark, ta hannun Shugaban Yankin, Mista Daniel Modu Bwala, da kuma shugabannin jam’iyyar a Jihar Gombe.

Ya ƙara da cewa, an kuma aika kwafin wasiƙar zuwa ga Shugaban ADC na Jihar Gombe da Shugaban Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Jam’iyyar na Ƙasa.

Sai dai, wasu majiyoyi sun sanar da cewa, tsohon kwamishinan na shirin komawa jam’iyyar APC mai mulki, domin mara wa ɗan takarar gwamnan jam’iyyar, Dr. Jamilu Isiyaku Gwamna, baya a zaɓen da ke tafe.

13/09/2026

Manchester United Ta Sha Ci Daya Mai Ban Haushi A Hannun City Har Gida, Duk Da Jan Kati Da Aka Baiwa City Din.

Minene Kuke Gani Matsalar Manchester United?

Photos from Hausa Digital RTV's post 13/09/2026

Ofishin Masari Ya Gana Da Malaman Addinin Musulunci Mata A Kaduna

Ofishin Mai Ba Shugaban Kasa Shawara Akan Harkokin Siyasa Alhaji Ibrahim Kabir Masari, Ya Gana Da Malaman Addinin Musulunci Mata A Jihar Kaduna.

Taron Ya Samu Shaidawar Gwamnoni Da Sauran Jiga-Jigan Masu Rike Da Mukamai Da Jagororin Jam'iyyar APC.

13/09/2026

"Mu A Karamar Hukumar Kaita Injiniya Bello Yandaki Da Jagororin Mu Sun Hadiye Duk Wani Dan Adawa".

"Kuma Babban Taron Mu Na Kungiyoyin APC Sama Da 4000 Ya Girgiza Jam'iyyun Adawa A Jihar Katsina".

Cewar Alhaji Nura Yandaki, Dan Jam'iyyar APC A Karamar Hukumar Kaita.

13/09/2026

Wasa Kwakwalwa.....

Nan Wane Wuri Ne A Cikin Birnin Katsina?

A Kafta.....

Photos from Hausa Digital RTV's post 12/09/2026

Dikko Youth Network Ta Fara Rangadin Kaddamar Da Shuwagabannin Ta Na Mazabu

Kungiyar yakin neman zaben Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda,PhD, da sauran yan takarar Jam'iyyar APC daga sama zuwa kasa, wato Dikko Youth Network, ta fara rangadin kaddamar da shuwagabannin ta na Mazabun Jihar.

Wakilin Hausa Digital RTV ya ruwaito cewa, yunkurin na da nufin karfafa tsarin yakin neman zaben Jam'iyyar APC a fadin Jihar.

Rangadin ya fara ne a yau, Asabar, 12 ga watan Satumba, 2026, a karkashin jagorancin Kakakin Majalisar Matasa ta Kasa, Rt.Hon.Aliyu Idris Zakari, inda tawagar ta kai ziyara kananan hukumomin Danmusa da Safana da Dutsinma da Kurfi.

A yayin rangadin, an kaddamar da jami'an Kungiyar na mazabu, a kananan hukumomin, tare da basu horo da dabarun da zasu taimaka wajen gudanar da ayyukan kungiyar a matakin gundumomi.

Hon.Aliyu Idris Zakari ya bayyana cewa, horon na da nufin shirya shuwagabannin domin shiga cikin harkokin wayar da kan jama'a da karfafa hadin kan matasa da kuma neman goyon baya da kuri'u ga Jam'iyyar APC a zabukan da ke tafe.

Rt.Hon.Aliyu Idris Zakari, ya bukaci sabbin shuwagabannin gundumomin da su kasance masu jajircewa da biyayya da kishin Jam'iyya, tare da gudanar da ayyukansu cikin tsari da mutunta al'umma.

Ya kuma jaddada muhimmancin matasa wajen tabbatar da nasarar Jam'iyyar APC a Jihar Katsina, yana mai cewa kungiyar zata cigaba da fadada ayyukanta zuwa sauran Kananan Hukumomi da gundumomin Jihar.

Photos from Hausa Digital RTV's post 12/09/2026

ADC A Shiyyar Daura.....

Ku Kalli Yadda Jam'iyyar ADC Ta Gudanar Da Babban Gangamin Kaddamar Da Yakin Neman Zaben Ta, A Shiyyar Dan Majalissar Dattawa Ta Daura, Jihar Katsina.

Ya Kuka Kalli Taron?

Photos from Hausa Digital RTV's post 12/09/2026

Ofishin Masari Ya Gana Da Manyan Malaman Jami'oi Na Arewacin Najeriya

Ofishin Mai Ba Shugaban Kasa Shawara Akan Harkokin Siyasa Alhaji Ibrahim Kabir Masari, ya gana da manyan malaman jami'oi na Arewacin Najeriya, akan batun nasarorin Gwamnatin Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu.

Taron dai ya kasance a matsayin wani zaure na tattauna batutuwa da s**a jibanci irin kokarin da Gwamnatin Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ta yi a bangaren ilimin gaba da sakadire.

Taron ya samu halartar manyan jami'an gwamnati, wanda s**a hada Ministan Gidaje Da Raya Birane Injiniya Muttaqa Rabe Darma da Karamin Ministan Tsaro Bello Matawalle.

12/09/2026

INNALILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN!!!

Allah Ya Yi Wa Alhaji Bamanga Tukur, Tsohon Shugaban Jam'iyyar PDP Na Kasa Rasuwa, A Gidan Shi Da Ke Birnin Tarayya Abuja.

Allah Ya Jikan Shi Da Rahama!

Photos from Hausa Digital RTV's post 11/09/2026

Gwanin Burgewa.....

Dan Majalissar Tarayya Mai Wakiltar Kananan Hukumomin Kankia/Ingawa Da Kusada Kenan, Hon.Abubakar Yahaya Kusada, Ya Ziyarci Gonar Shi.

📸: Mobile Media Crew

Want your business to be the top-listed Media Company in Katsina?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Website

Address

Katsina
820001

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Hausa Digital RTV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Subscribe

We will notify you when anything happens in Katsina.