Katsina State Community Development Programme

Katsina State Community Development Programme

Share

Office of the State Coordinator, Katsina State Community Development Programme (KSCDP).

19/09/2026

Shugaban Shirin Ci gaban Al’umma, Assoc. Prof. Kamaluddeen Kabir, ya ƙaddamar da rabon tallafin manyan buhunan shinkafa ga al’ummar gundumomi 12 da muke da su a Ƙaramar Hukumar Katsina, kamar yadda Mai Girma Gwamna, Malam Dikko Umar Radda, ya bayar da umarni.

19/09/2026

Shugaban Shirin Ci gaban Al’umma, Assoc. Prof. Kamaluddeen Kabir, ya kai ziyarar gani da ido a Gundumar Wakilin Gabas (II), domin duba yadda ake tantance sunayen mutanen da za su amfana da tallafin babban buhun Shinkafa, Hatsi, Masara da kuma Dawa da Mai Girma Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda, ya bayar domin a raba wa al’umma a dukkanin gundumomi 361 da ke faɗin Jihar Katsina.

19/09/2026

Tattaunawar Shugaban Shirin Ci gaban Al’umma, Assoc. Prof. Kamaluddeen Kabir, tare da Wakilin Masu Buƙata ta Musamman na Gundumar Wakilin Kudu (I), a yayin ziyarar gani da ido da Shugaban ya kai wajen tantance mutanen da za su amfana da tallafin babban buhun shinkafa, wanda Mai Girma Gwamna Malam Dikko Umar Radda ya bayar domin a raba wa gundumomi 361 da ke faɗin Jihar Katsina.

18/09/2026

GIREMAWA WARD, BINDAWA LOCAL GOVERNMENT

Al'ummar Gundumar Giremawa, sun shaida amsar saƙon su, hannu da hannu daga mai girma Gwamnan Jihar Katsina Mal. Dr. Dikko Umaru Radda ta hannun Shugaban Shirin Cigaban Al'umma daga Tushe (CDP) Assoc. Professor Kamaluddeen Kabir Katsina.

Idan ba a manta ba, ana cigaba da rabon hatsi a dukkanin Gundumomin 361 dake a Jihar Katsina, a bisa umarnin Mai girma Gwamnan Jihar Katsina domin a ba al'umma mabuƙata.

17/09/2026

An fara Saka 10M Naira a Asusun CLC's na Wards. Kashi na biyu.
Ku Ziyarci Ofisoshin CDP na Gundumomin ku, domin ba da ayyukan da ku ke so a yi maku.

Photos from Katsina State Community Development Programme's post 17/09/2026

HANNU DA HANNU 🤝

Saƙon Mai Girma Gwamna, Malam Dr. Dikko Umaru Radda, lungu da saƙo.

16/09/2026

Jagororin Ƙungiyar Masu Buƙata Ta Musamman mai taken suna Coalition of Katsina State Disability Group, ƙarƙashin jagorancin Hon. Umar Jibril Bindawa (S.A. to the Governor on Disabled Matters, Katsina State), sun kawo ziyarar ban-girma da girmamawa ga Shugaban Shirin Ci gaban Al’umma (CDP), Assoc. Prof. Kamaluddeen Kabir.

A yayin ziyarar, jagororin ƙungiyar sun yaba da ƙoƙari da jajircewar shugaban wajen tabbatar da cewa saƙon Mai Girma Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Radda, yana isa ga al’umma, musamman waɗanda ke ƙasa daga tushe.

Haka kuma, sun yaba da yadda Shirin Ci gaban Al’umma (CDP) ke ba mutane masu buƙata ta musamman muhimmanci a cikin ayyukansa, tare da tabbatar da cewa suna amfana da kayayyaki da tallafin da ake rabawa.

A ƙarshe, jagororin ƙungiyar sun miƙa wa Shugaban CDP, Assoc. Prof. Kamaluddeen Kabir, lambar yabo ta girmamawa bisa ƙoƙarinsa, jajircewarsa da gudummawar da yake bayarwa wajen gudanar da ayyukan ci gaba a faɗin Jihar Katsina.

Photos from Katsina State Community Development Programme's post 16/09/2026

13/09/2026

YANGORA WARD, BINDAWA LGA

Shugaban Shirin Cigaban Al'umma (CDP) Assoc. Professor. Kamaluddeen Kabir Katsina ya jagoranci jami'an hukumar domin raba tallafin hatsi da mai girma Gwamna Mal. Dr. Dikko Umaru Radda PhD CON ya bada umarnin a rabawa al'umma mabuƙata a Yangora Ward dake karamar hukumar Bindawa.

Tawagar ta samu rakiyar shugaban ƙaramar hukumar Bindawa, Hon. Badaru Musa Giremawa tare da jama'ar sa.

Want your organization to be the top-listed Government Service in Katsina?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Website

Address

Katsina

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Katsina State Community Development Programme posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Subscribe

We will notify you when anything happens in Katsina.