Muhammad UMC
Muhammad Ghaddafii D Alhassan. official page. Allah ya ƙarawa Annabi daraja
Masha Allah 🙏
07/06/2026
Idan ka zalunci wani don kafi ƙarfinsa, wata rana wani zai zalunceka don yafi ƙarfinka.
06/06/2026
Tsanani ba zai daɗe ba, ƙunci ba zai tabbata har abada ba, bayan dare akwai alfijir,
kuma haƙuri yana daga cikin mafi kyawun ibadu, Addu'a kuwa tana karya damuwa da baƙin ciki.
Idan ka ce:- "Ya Ubangiji!"
to ko dai ya amsa maka kiranka, ko ya kau da wata musiba daga gare ka, ko kuma ya rubuta maka lada a ɓoye.
Ya Allah, muna roƙonka da ka ba mu mafita kusa, wadda za ta faranta zukata,
ta yaye damuwa da ƙunci, ta kuma sanyaya zukata da natsuwa.
Click here to claim your Sponsored Listing.