General BMB
African Actor | Film Director | Influencer My name is Bello Mohammad Bello (General BMB)
An ce Malam ya yi order na Alkur’ani. Nace, saukar Alƙur’ani za'ayi, ko kuwa akwai wani shiri na daban da ba mu sani ba?
Yanzu, yaya makomar Jam’iyyar PDP a idon Malam? Ta koma “alkafira” ne, ko kuwa an riga an yi mata stamp ta zama halastacciya? 🤔
25/09/2026
Jam’iyyar APC ta yi raraka, ita ma PDP ta yi nata rarakar. 😅
Yanzu ya za a yi kenan? Ko dai ADC za a koma? 🤔
Au, na tuna! Mai sunana yana nan a wannan waje — ina nufin BBT, wato Bala Bello Tinka.
Ko zai yi wa tasa jam’iyyar rajista ne yayama sunan ta🙄?
25/09/2026
Alhamdulillahi Rabbil Alamin. Wassalatu wassalamu ala Rasulillahi Muhammadin wa ala alihi wa sahbihi ajma’in.
Ya ku bayin Allah, ku ji tsoron Allah, ku kyautata niyyarku, ku kiyaye harshenku, kuma ku kyautata mu’amalarku da juna. Rayuwa gajera ce, abin da zai rage wa mutum shi ne ayyukan alheri.
Mu kasance masu gaskiya, hakuri, yafiya da tausayi. Kada bambancin ra’ayi ya raba zukatanmu, domin dukkanmu ‘yan Adam ne, kuma muna bukatar rahamar Allah.
Allah Ya shiryar da mu, Ya gyara zukatanmu, Ya gafarta mana zunubanmu, Ya ba mu zaman lafiya da albarka a duniya da lahira.
Allahumma’ghfir lana warhamna, wahdina wa aslih ahwalana.
Allahumma ati-na fid-dunya hasanah, wa fil-akhirati hasanah, wa qina ‘adhaban-nar.
Wasallallahu ala Sayyidina Muhammadin wa ala alihi wa sahbihi ajma’in.
Amin Ya Rabbal Alamin.
25/09/2026
Jumu'ah Mubarak, Ya Ahibba'a Muhammadur Rasulullah.💚
24/09/2026
Ba na tare da Isa Ali Pantami a siyasa, amma ba zan bari bambancin ra’ayi ya hana ni faɗin abin da na ga ya dace ba.
Idan aka ce za a sake primary a jam'iyyar PDP na jihar Gombe, to wannan ba ƙarshen tafiyar Pantami ba ne, kuma ba tabbacin nasararsa ba ne.
Idan Pantami yana da ƙarfin da magoya bayansa suke ikirari, sabon primary zai ba shi damar sake tabbatar da hakan. Idan kuma wani ya fi samun goyon bayan ’yan jam’iyyar, shi ne zai samu tikitin.
Abin da ya kamata mu guje wa shi ne amfani da siyasa wajen murɗe gaskiya. Ba lallai ka goyi bayan mutum ba kafin ka yi masa adalci.
Yanzu primary za ta sake zama kotun ’yan PDP. Mu ga wanda kuri’ar cikin gida za ta zaɓa. 👀
24/09/2026
Ultra Wallet sun turo min $6 a matsayin reward. 👌🏻
Masu sha’awar gwadawa za su iya shiga su duba yadda yake. An kuma sanar da cewa za a fara P2P a cikin wallet ɗin a ranar 1 ga October.
Link ɗin yana cikin comments 👇🏻
24/09/2026
Jan kunne da nasiha ga masu amfani da AI wajen ƙirƙirar irin waɗannan abubuwa.
Alƙur’ani ba abin wasa ba ne, kuma bai dace a yi amfani da shi wajen neman likes, comments ko views ta wannan siga ba. Yin hotunan da ke nuna Alƙur’ani mota tayi hatsari rashin girmama Allah ne. Yin hakan bai dace da darajar Littafin Allah ba.
Mu riƙa amfani da fasaha cikin ilmi, hankali da girmamawa. Allah Ya shiryar da mu. 🤲🏻
What is happening!?
24/09/2026
القرآن نور الدنيا
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Website
Address
Plateau
Jos
930001