Muryar Raunana

Muryar Raunana

Share

Muryar Raunana is for Broadcasting News, articles and General update not only related to Nigeria, but the World in general.

10/08/2026

BABI NA DAYA: Labarin Kayataccen Littafi Mai Suna 'KADDARA KO SOYAYYA'

Karanta anan👇👇
https://www.facebook.com/share/1DF7Ftz8LK/

ƘADDARA KO SOYAYYA?

BABI NA ƊAYA

Kashi na Ɗaya: Mafarkin Da Bai San Makomarsa Ba

"Lalle ne tare da tsanani akwai sauƙi." (Suratul Inshirah: 6).

Safiyar ranar Litinin ce.

Iskar hunturu mai sanyi tana kaɗawa a garin Soba, yayin da hasken alfijir ya fara bayyana daga gabas. Tsuntsaye suna tashi daga bishiyoyi suna rerawa baitoci cikin nutsuwa, alamar sabuwar rana ta fara.

A wani gida mai cike da tsafta, ana iya jin ƙarar famfon ruwa yana zuba.

Shi ne gidan Malam Mahadi Mafatihu, tsohon malami kuma mutum mai tsoron Allah wanda ya shahara da gaskiya da riƙon amana.

A cikin gidan ne ɗansa kaɗai namiji, Journalist Muhammad, yake zaune.

Tun yana ƙarami mutane suke cewa:

"Wannan yaron yana da nutsuwa fiye da shekarunsa."

Muhammad ba ya son hayaniya ko zaman banza. Duk wanda ya san shi ya san yana fara ranarsa da sallar Asuba a masallaci, sannan ya zauna yana karatun Alƙur'ani kafin ya fara ayyukansa.

A wannan safiyar ma haka abin ya kasance.

Bayan dawowarsa daga masallaci, ya shiga banɗaki ya yi wanka. Tsabta tana daga cikin abubuwan da ba ya wasa da su. Sau da dama abokansa s**an yi masa raha.

"Wai Muhammad, sau nawa kake yin wanka a rana ne?"

Sai ya yi murmushi ya ce,

"Idan Allah Ya ba mutum lafiya da ruwa, me zai hana ya kasance cikin tsafta?"

Bayan ya gama shiryawa, ya sanya farar doguwar riga mai tsafta, ya ɗaura hularsa, sannan ya ɗauki turarensa ya fesa.

Ya tsaya a gaban madubi.

Ba wai saboda girman kai ba.

Sai don ya tabbatar komai yana cikin tsari.

Daga ɗakinsa ya fito yana ɗauke da jakar aikinsa da kyamarar daukar hoto.

A daidai lokacin mahaifinsa yana zaune a farfajiyar gida yana shan shayi.

"Assalamu Alaikum, Abba."

"Wa Alaikumus Salam, Muhammad."

"Yau akwai wani babban taron addini a Zariya. Gidan jarida ya aike ni domin ɗaukar rahoto."

Malam Mahadi Mafatihu ya gyara zama.

"Allah Ya ba ka sa'a."

"Amin."

Sai ya ƙara da cewa,

"Ka tuna, ɗana. Aikin jarida amana ne. Kada ka rubuta abin da ba ka gani ba. Kada ka zalunci kowa saboda son labari."

Muhammad ya gyada kai.

"Na riƙe wannan nasiha tun farko, Abba."

Malam Mahadi Mafatihu ya yi murmushi.

"Wannan shi ne abin da ya sa nake alfahari da kai."

Muhammad ya durƙusa ya sumbaci hannun mahaifinsa kafin ya nufi mota.

A gefe guda kuma...

A cikin tsohon unguwar Gyallesu da ke cikin garin Zariya, wata budurwa tana tsaye a gaban madubi tana gyara baƙin hijabinta.

Sunanta Zahra Alhaji Ali Usman Nayara.

Ba kyawunta ne ya fi ɗaukar hankalin mutane ba.

Abin da ya fi jan hankali shi ne kamun kanta.

Tun tana makarantar sakandare ta saba sanya baƙaƙen dogayen kaya masu rufe jikinta gaba ɗaya tare da baƙin hijabi dogo har ƙasa.

Mahaifiyarta, Hajiya Maryam, ta shigo ɗakin.

"Kin shirya ne?"

"Eh, Umma."

"Yau ma aikin jarida kenan?"

Zahra ta yi murmushi.

"Eh. An ce manyan malamai daga jihohi daban-daban za su halarci taron. Ana son mu tattara cikakken rahoto."

Hajiya Maryam ta gyara mata gefen hijabi.

"Kada ki manta..."

Zahra ta ƙarasa maganar cikin murmushi.

"...Mutuncin mace shi ne kayan adonta."

Mahaifiyarta ta yi dariya.

"Ashe har yanzu kina tunawa."

"Ba zan manta da abin da kika koya mini ba."

Hajiya Maryam ta rungume ƴarta.

"Allah Ya tsare ki."

"Amin."

A falon gida kuwa...

Alhaji Ali Usman Nayara yana karanta jarida.

Ya ɗaga kai ya kalli Zahra.

"Ƴata."

"Na'am, Baba."

"Na ji ana yawan yabon rubuce-rubucenki."

Zahra ta sunkuyar da kai cikin kunya.

"Duk da taimakon Allah ne."

Ya yi murmushi.

"Ki ci gaba da kare gaskiya. Ɗan jarida na gaskiya ba ya sayar da mutuncinsa saboda kuɗi."

"In sha Allah, Baba."

Ya ɗauko walat daga aljihu ya ba ta kuɗin mota.

"Allah Ya kiyaye."

Ta karɓa tana godiya.

A daidai lokacin...

Muhammad ya iso Zariya.

Ya faka motarsa a kusa da filin taron.

Jama'a sun cika ko'ina.

An kafa tantuna.

Masu ɗaukar hoto suna ta kai-komo.

Masu gabatar da shirye-shirye suna gwada na'urorin sauti.

Masu aikin tsaro suna tsara shigar baƙi.

Muhammad ya rataya katin aikinsa a wuya.

Ya ɗauki kyamararsa.

Ya ja dogon numfashi.

Bai san cewa wannan rana ce za ta sauya rayuwarsa har abada ba.

A wani ɓangaren filin taron kuma...

Zahra ta iso tare da takwarorinta.

Ta rataya katin aikin jarida a wuya.

Ta buɗe ƙaramin littafin rubutu da alƙalami a hannunta.

Ba ta san cewa yau ne za ta haɗu da mutumin da zuciyarta za ta zaɓa ba.

Kuma ba su san cewa wannan haɗuwar za ta jefa su cikin jarabawar da za ta gwada haƙurinsu, imaninsu da soyayyarsu ba.

📖 Za a ci gaba...

A KASHI NA BIYU: Shin ya haɗuwar Muhammad da Zahra zai kasance, wani rahoto za su haɗa, imani zai yi rinjaye ko soyayya?.

Mu haɗu a kashi na biyu ranar Juma'a da misalin karfe 7:30 na Dare a shafin DA'IRAR ZARIYA https://www.facebook.com/DairarZaria

©️Zaria Media Forum
26/Safar/1448H
10/08/2026

08/08/2026

SABON LITTAFI: Labarin Kayataccen Littafi Mai Suna 'KADDARA KO SOYAYYA'

Mu na farin cikin sanar da ma su bibiyan mu cewa za mu ke kawo mu ku Labarin Kayataccen Littafi Mai Suna 'KADDARA KO SOYAYYA'.

Labari rayuwa ta gaskiya tsakanin ƴan jarida biyu Muhammad da Zahra, wacce ta fuskanci kalubale talauci, son zuciyar dangi, kishi, makirci da jarabawar rayuwa.

Labari mai kunshe da:
1. Soyayya
2. Imani
3. Gaskiya
4. Gwagwarmaya
5. Hakin mace
6. Tarbiyya
7. Dogaro ga Allah

DARUSSAN LABARIN:
▪️Soyayya ta gaskiya tana ginuwa ne a kan amana, mutuntawa da tsoron Allah.
▪️Kyakkyawar tarbiyya da cikakken shigar Musulunci abin alfahari ne ga namiji da mace.
▪️Bai dace a tilasta wa mace auren wanda ba ta so ba.
▪️Dukiya ba ita ce ma'aunin nagartar miji ba; addini da kyawawan halaye sun fi muhimmanci.
▪️Haƙuri, addu'a da dogaro ga Allah s**an buɗe ƙofofin mafita idan ƙalubale sun yi yawa.
▪️Iyayen da suke sauraron ra'ayin 'ya'yansu cikin hikima s**an taimaka wajen gina iyalai masu ɗorewa.

Za mu ke wallafa labarin a ranakun:
Litinin – 7:30 na Dare
Juma'a – 7:30 na Dare
Lahadi – 7:30 na Dare

Labarin zai ke zuwa mu ku a shafin DA'IRAR ZARIYA https://www.facebook.com/DairarZaria

RUBUTAWA:
Shamsudeen Adamu Alshirazy da Azzahra Muhammad

©️Zaria Media Forum
24/Safar/1448H
08/08/2026

Photos from ABS Radio Hausa's post 12/06/2026

ISMA Ta Shiga Mu’utamar Na Kasa Karo Na 28 A Abuja

A yau Juma’a, 12 ga Yuni, 2026, Dandalin kula da lafiya na Harkar Musulunci, ISMA Medical Care Initiatives, ƙarƙashin jagorancin Sheikh Ibraheem Zakzaky(H), ta fara gabatar da gagarumin taron ƙara wa juna sani na ƙasa karo na 28 (28th ISMA National Seminar 2026) a Kuje dake babban birnin tarayya, Abuja.

Masana da ƙwararrun ma’aikatan lafiya daga sassa daban-daban na ƙasar za su gabatar da muhimman bayanai da s**a shafi bunƙasa harkokin kiwon lafiya da kuma samar da mafita ga ƙalubalen da al’umma ke fuskanta.

Taken Taron:
“Ta’ammuli da Miyagun Ƙwayoyi a Tsakanin Matasan Najeriya: Barazanar Hakan ga Lafiya, Illolinsa ga Zamantakewa da Kuma Hanyoyin Samar da Mafita.”

📸 Kabiru Adamu Soba

©ABS Radio Hausa

https://www.facebook.com/share/1Cw8MNE6WN/

08/06/2026

GÃ-ZÃ DA MATSIN RAYUWA:

Mahukuntan haramtacciyar ƙasar Izrãilå sun rufe dukkan hanyoyin shiga da fita na kan iyakar Gã-zã tare da dakatar da shigar da kayan agajin jin ƙai zuwa yankin, duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da ake cewa ta samu goyon bayan Ãmurk-ã.

Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da kakaba takunkumi da kai hare-hare, lamarin da ke ƙara tsananta matsalar jin ƙai tare da jefa al'ummar Fãl-åsɗinu a Gã-zã cikin mawuyacin hali.

—Muryar Raunana

08/06/2026

Haramtacciyar Kasar Izrãilå na ci gaba da ayyukan ta'addanci a Gã-zã‼️

📷 08.06.2026
Birnin Gã-zã

—Muryar Raunana

08/06/2026

A cewar Ma'aikatar Lafiya ta Gã-zã:

▪️ Mutane 9 sun yi shahada, yayin da wasu 43 s**a jikkata, bayan an kai su asibitocin da ke faɗin Zirin Gã-zã cikin awanni 24 da s**a gabata.

▪️ Tun bayan fara yarjejeniyar tsagaita wuta (11 ga Oktoba):
Jimillar waɗanda s**a yi shahada: 970
Jimillar waɗanda s**a jikkata: 3,063
Adadin gawarwakin da aka ciro daga ƙarƙashin baraguzan gine-gine: 782

▪️ Jimillar alƙaluman yaƙin zuwa yanzu:
Adadin waɗanda s**a yi shahada: 72,980
Adadin waɗanda s**a jikkata: 173,171.

—Muryar Raunana

08/06/2026

A Yau, An kuma sake yanke wani ɓangare na ƙafar jariri Muhammad Al-Khatib. Jaririn bai wuce kwanaki 40 da haihuwa ba.

Wannan na daga cikin irin munanan abubuwan da yaƙin ta'addancin haramtacciyar Kasar Izrãilå a Gã-zã ke jefa yara marasa laifi cikin su, inda suke fuskantar raunika masu tsanani da rasa gabobin jikinsu tun suna jarirai.

— Muryar Raunana

Photos from Muryar Raunana's post 08/06/2026

Ƴan uwa da al'ummar Fälãsɗinû sun gudanar da jana'izar matashin nan mai shekaru 16, Abbas Mohammed Abu Jabal, a Asibitin Al-Shifa da ke birnin Gã-zã, bayan da ya yi shahada sakamakon harin sama da sojojin mamayar Izrãilå s**a kai kan wata mota a cikin birnin a daren jiya.

— Muryar Raunana

08/06/2026

Inna-lillahi wa Inna ilaihi rajiun 💔 😭

A yau Litinin 8 ga watan Yuni muke cika kwanaki 100 cur da Shahadar Shugaban Musulman duniya, Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci, Shugaban Shahidan Ƙarni Ayatollah Uzama Ash-shahid Sayyid Ali Hussaini Khamene'i(Rahimahullah).

Allah ya sabunta rahmarsa agareka ya shugabah, ka barmu da gangan jiki amma ambatonka da ayyukan na cigaba da wanzuwa.🕊️💐💔

Want your business to be the top-listed Media Company in Kaduna?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Website

Address


Soba
Kaduna