Els4k

Els4k

Share

Influencer

07/07/2026
07/07/2026

Arewa tafi kudu ilimi - Prof. Abdullah Uba Adamu

14/06/2026

Hmmm

30/05/2026

DALILAI UKU NE YASA MUTANEN KUDU SUKE ZAGIN DR AHMAD GUMI.

A kwana kwanan nan ana yawaitar samun wallafa labarai na ƙage da kokarin muzantar wa daga mutanen kudancin Najeriya har ma da wasu wawaye daga Arewacin Najeriya, musamman dangane da abunda ya shafi zargin Ta'addanci da kuma alaƙa da ƴan bindigar daji wanda hakan yayi munmunan tasiri a zukata wasu da dama a kudancin najeriya harma da arewaci.

Bisa nazari da nayi da kuma fahimtar hakikanin dalilan da yasa masu yada irin waɗanann labarai ke yin hakan baya rasa nasaba saba da abubuwa guda Uku.

Na farko shine haushin su na Hukuncin dauri rai da rai ga Shugaban ƴan ta'addan IPOB da Gwamnatin Najeriya tayi a kwanaki baya wanda idan baku manta ba tun kafin a zartar masa da hukunci dama suna yawan kiraye kirayen cewa Gwamnati ta k**a Sheikh Gumi domin zargin da sukeyi masa na ta'addanci. Tun bayan Hukuncin da Gwamnatin tarayya tayi naga su mutanen kudancin najeriya da dama sannan sun wallafa a shafukan su na sada zumunta cewa Gwamnatin najeriya ta k**a Shugaban kungiyar Ta'addanci na IPOB ta kulle Saidai taki k**a Sheikh Gumi. to daga nan ne Wadannan abubuwa s**a fara taso wa na dauko karatu karatuttuka da Sheikh Gumi yayi harda na shekaru da s**a wuce suke datsan maganganun sa domin suyi amfani dasu a matsayin makami a kafar sada zumunta don tabbatar wa da duniya cewa ai yanada alaka da ta'addanci. tunanin su yin hakan shine zai sa Gwamnatin Najeriya ta k**a Sheikh Gumi ta daure shi k**ar yanda tayiwa Shugaban su na kungiyar ta'addanci ta IPOB.

Abu na 2 shine Kokarin da Sheikh Gumi keyi na haskawa mutanen Arewacin Najeriya hakikanin Masu daukar nauyin ta'addanci musamman a Arewacin Najeriya da kokarin shawo kan matsalar Fulani makiyaya wanda aka zalunta Har Sheikh Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi yake ganin yin sulhu da ƴan bindigan daji zai kawo karshen matsar da yin adalci cikin daji shine basu so, domin sun san tabbas idan har Sheikh Gumi yayi nasara Wajen shawo bakin zaren to tabbas matsalar tsaro a Arewa na iya zama tarihi , sukuma masu amfana da rashin zaman lafiyan kasuwar su zata mutu.
shiyasa suke yin duk mai yiwuwa wurin ganin sun Aibata Sheikh Gumi domin a daina ganin k**ar sa a kasar baki daya.

A gefe guda kuma sun manta Ra'ayin Sheikh Gumi na yin Sulhu da ƴan bindiga shine Ra'ayin Peter Obi dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NDC ,wanda kwanaki baya ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa bai goyi bayan Hukuncin da Gwamnatin Najeriya ta yanke wa Shugaban Kungiyar Ta'addanci ta IPOB wato Nnamdi Kanu ba, yace yana ganin yin Sulhu dasu shine mafita, Amma dake shine shafa feel da mai basa zargin shi da Ta'addanci sai Sheikh Gumi.

Abu na 3 shine Kau da hankalin mutanen Najeriya daga zargin masu daukar nauyin Ta'addanci a kasar da nuna wa mutane cewa Sheikh Gumi ne shugaban su - domin dukkan su masu zargin Sheikh Gumi idan kun kula Akwai munmunar kiyayyar musulunci a tare dasu , kuma dama kullum su burin su shine tabbatar wa da duniya cewa musulmi ƴan ta'adda ne , Kuma tunda Sheikh Gumi musulmi ne tohakan ya basu damar yin hakan domin su kara batawa musulunci suna a idon Duniya. Saidai bazasuyi nasara ba.

Sukuma daga cikin mutanen Arewa da suke biye musu ni ina daukan su wawaye ne, basu ma san inda duniya ta dosa ba, domin dayawan su ana amfani da kabilanci ne wurin cusa musu kiyayyar Fulani saboda laifin wasu tsirara daga cikin su. Muna fata Allah ya dawo mana da zaman lafiya a Arewacin Najeriya yayi mana Maganin dukkanin damuwa , Ameen.

17/05/2026

💔💔

13/05/2026

"Makaryata Bazasu Shiga Aljannaba" ~ Sowore ya Cacchaki, Kwankwaso : Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa kuma jagoran jam'iyyar AAC, Omoyele Sowore, ya soki tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, kan furucinsa cewa ɗiyarsa ce ta taɓa ba shi shawarar wanda zai yi aiki tare da shi a zaɓen 2027.

Acikin wani sako da Sowore ya wallafa, ya ce idan har ɗiyarsa ce ke ba shi shawarar wanda zai marawa baya a 2027, to ya k**ata ace ita ce ta tsaya takarar shugaban ƙasa, yana mai cewa hakan na nuna Kwankwaso ba shi da ƙwarewar siyasa.

Sowore ya kuma zargi Kwankwaso da yin ƙarya, inda ya ce “maƙaryata ba za su shiga aljanna ba,” a ƙarshen saƙonsa...

Shin Me za kuce?..

27/04/2026

Mabiyana na Instagram, An rufe min account dina Amma ga Sabon da na Bude yanzu, Nagode🙏Nasaka link a Comment Section 👇

26/04/2026

Yadda aka sake samun wani mummunan hatsari a titin Nnamdi Azikiwe (Bypass), kusa da kasuwar Sabuwar Fanteka.

Inda wata babbar motar trailer ta buge wasu matasa biyu da ke kan babur, kuma nan take s**a rasu.

Lamarin dai ya tayar da hankalin jama’a, inda wasu fusatattun matasa s**a mayar da martani ta hanyar ƙona motar trailer ɗin nan take.

Yak**ata Gwamnatin Jihar kaduna ta duba lamarin titin bypass na kaduna duba da yanda ake kara samun rashe rashen rayuka.

26/04/2026

Inada Kwarin Giwar cin zaben 2027 - Gwamna Abba

Want your public figure to be the top-listed Public Figure in Kano Outlying?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Website

Address


Kano Outlying

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Els4k posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Subscribe

We will notify you when anything happens in Kano Outlying.