Harafi Plus
Harafi Masomin Kalma, Harafi Tashar Amanna
22/01/2026
Wani lauya a Jihar Kano, Mubarak Abubakar, ya ce kiran da ake yi kan a gaggauta kashe waɗanda aka k**a bisa zargin kashe wata uwa da ’ya’yanta shida a unguwar Dorayi-Chiranci, ba daidai ba ne kuma ya saɓa wa tsarin shari’ar laifuka na Najeriya.
Yayin da yake bayani daga mahangar shari’a, lauyan ya ce ba za a iya aiwatar da hukuncin kisa ga kowa ba sai kotu mai ikon yanke hukunci ta same shi da laifi.
31/12/2025
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sanya hannu kan kasafin kuɗin shekarar 2026 na Naira tiriliyan 1.477.
Bayan sanya hannu kan kasafin, Gwamna Abba, ya yi kira ga mambobin majalisar zartarwa su ƙara jajircewa wajen cimma burin gwamnati.
Ya nuna cewa kasafin shekarar 2025 ya samu nasarar aiwatar da sama da kashi 80 cikin 100, musamman a fannin ilimi, lafiya, da manyan ayyukan ci gaba.
23/12/2025
Takaddama mai zafi ta dabaibaye sabbin dokokin haraji da Majalisar Dokoki ta Ƙasa ta amince da su, bayan zarge-zargen cewa an yi sauye-sauye a cikin dokokin ta bayan fage, bayan an kammala dukkan matakan amincewa da su a majalisa.
Batun da ya taso ya jawo cece-kuce daga ’yan majalisa, jam’iyyun adawa da ƙungiyoyin fararen hula, inda suke tambayar sahihancin abin da aka miƙa wa Fadar Shugaban Kasa domin aiwatarwa.
Masu s**a na cewa sauye-sauyen da ake zargin an yi ba tare da amincewar majalisa ba na iya lalata tsarin dimokuraɗiyya, tare da haifar da rashin gaskiya da riƙon amana a tsarin dokoki.
A ɗaya bangaren kuma, Fadar Shugaban Ƙasa ta yi nuni da cewa abin da aka yi gyara ne na fasaha da tsari, ba sauya ma’anar doka ba.
Matashi ɗan Arewacin Najeriya da ya ƙirƙiri samfurin makamin rocket.
Rundunar Yan Sandan Kano ta magantu akan iftila'in da ya faru a unguwar Hotoro
Harafi Plus, Harafi masomin kalma, Harafi tashar amanna.
12/12/2025
Ministocin Buhari da EFCC ke bincika
Rahotanni na bayyana cewa hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci na tsare da tsohon gwamnan jihar Anambra kuma tsohon ministan ƙwadago, Chris Ngige.
Ɗaya daga cikin tsofaffin masu magana da yawunsa, Fred Chukwuelobe, ya tababatar da cewa Ngige na hannun hukumar.
Sai dai EFCC ba ta tabbatar da tsarewar ba, sannan kakakin hukumar Dele Oyewole bai amsa saƙonnin da manema labarai s**a aike masa ba game da batun.
Mista Ngige ne na baya-bayan nan da EFCC ke bincike cikin tsofaffin ministoci da manyan jami'an gwamnatin marigayi Shugaba Muhammadu Buhari game da cin hanci.
06/12/2025
"Mai girma Gwamnan Jahar Kano, Alh Abba Kabir Yusuf zai tsunduma wasu daga cikin matasa cikin alkhairi ta ƙarƙashin ofishina, nan bada jimawa ba in sha Allah. Duk Wanda Allah yasa ya rabauta musamman kana da rabo da kuma zuciya zaka iya zama CEO. Allah ya albarkaci matasan jahar Kano. Amen ya Allah" – Shaddadu Danjuma Aliyu
Menene falalar dake cikin kiwon zuma?
27/11/2025
Majalisar Wakilai a ranar Alhamis, ta bukaci Gwamnatin Tarayya da ta yi amfani da diflomasiyya da duk wasu hanyoyi don tabbatar da dawowar tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan lafiya daga Guinea Bissau, bayan juyin mulkin sojoji a ƙasar.
Wannan kuduri ya biyo bayan amincewa da kudurin gaggawa da Shugaban Masu Rinjaye na majalisar, Farfesa Julius Ihonvbere, ya gabatar.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Website
Address
116 New Court Road, Gyadi-Gyadi
Kano
700233
Opening Hours
| Monday | 09:00 - 17:00 |
| Tuesday | 09:00 - 17:00 |
| Wednesday | 09:00 - 17:00 |
| Thursday | 09:00 - 17:00 |
| Friday | 09:00 - 17:00 |
| Saturday | 09:00 - 17:00 |
| Sunday | 09:00 - 17:00 |
Alerts
Be the first to know and let us send you an email when Harafi Plus posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.