AMR Hausa

AMR Hausa

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from AMR Hausa, Journalist, Zawachiki, Kano.

An kirkir wannan shafi na AMR Hausa don sanar da ku halin da Duniya ta ke ciki, ta hanyar samar muku da sahihan Labarai da Rahotoni a gida Nigeria da Afrika da sauran sassan Duniya.

Photos from AMR Hausa's post 21/09/2026

Gwamnatin Jahar Kano Za Ta Fara Faɗaɗa Rarraba Ruwa Cikin Mako Guda.

Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa ana sa ran fara faɗaɗa rarraba ruwan sha ga al’ummomi a faɗin jihar cikin mako guda, yayin da ayyukan gyaran manyan cibiyoyin samar da ruwa s**a kusa kammala.

Kwamishinan Albarkatun Ruwa, Muhalli da Sauyin Yanayi na Jihar Kano, Dr. Dahiru Muhammad Hashim, ne ya bayyana hakan yayin wata hira da Freedom Radio, inda ya ce ayyukan da gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf ke gudanarwa sun samu gagarumin ci gaba.

A cewar Kwamishinan, manyan wuraren samar da ruwa da s**a haɗa da Challawa Water Treatment Plant, Tamburawa Water Treatment Plant da Goron Dutse Reservoir, da kuma wasu tsare-tsaren samar da ruwa na yankuna, suna dab da komawa aiki yadda ya k**ata.

Ya ce ana sa ran fara gwajin tsarin da kuma faɗaɗa rarraba ruwa a cikin kwanaki masu zuwa, domin al’ummomin da s**a daɗe suna fama da ƙarancin ruwa su fara samun ruwan sha mai tsafta.

Daga cikin ayyukan da aka gudanar akwai gyaran layukan rarraba ruwa, ciki har da muhimmiyar hanyar ruwa mai tsawon kilomita 15.6 zuwa Goron Dutse, da kuma aikin cire laka da gyaran tafkunan ruwa da ke da jimillar ƙarfin sama da lita miliyan 40.

Haka kuma, an gyara wasu famfunan ruwa da na’urorin tace ruwa, tare da farfaɗo da wasu tsare-tsaren samar da ruwa na yankuna da s**a daɗe ba sa aiki, ciki har da Guzu-Guzu, Joda da Thomas.

Ma’aikatar ta bayyana cewa daga cikin tsare-tsaren samar da ruwa na yankuna guda 19 da ke jihar, tara na cikin aikin farfaɗowa, yayin da wasu daga cikinsu s**a riga s**a fara samar da ruwa bayan shekaru suna zaman kashe aiki.

Dr. Hashim ya ce matakan da ake ɗauka na daga cikin babbar manufar gwamnatin jihar ta rage gibin ruwa da ake fuskanta a Greater Kano, wanda aka kiyasta ya haura lita miliyan 300 a kowace rana.

Ya kuma jaddada buƙatar kare kayan aikin samar da ruwa daga lalacewa, satar kayan aiki, lalata ababen more rayuwa da kuma haɗa bututun ruwa ba bisa ka’ida ba, domin tabbatar da cewa ayyukan da aka gyara za su ci gaba da amfanar al’umma cikin ɗorewa.

A wani ɓangare kuma, Kwamishinan ya bayyana cewa gwamnatin jihar na ci gaba da wasu shirye-shiryen kare muhalli, musamman inganta harkokin kwashe shara, samar da kayan kariya ga ma’aikatan tsaftar muhalli da haɗin gwiwa da masu ruwa da tsaki domin samar da al’umma mai tsafta da juriya ga matsalolin muhalli.

Gwamnatin ta buƙaci mazauna Kano da su ba da haɗin kai wajen kare kayayyakin samar da ruwa tare da kai rahoton duk wani aikin lalata ababen more rayuwa ko haɗa ruwa ba bisa ƙa’ida ba.

Ana sa ran Ma’aikatar Albarkatun Ruwa, Muhalli da Sauyin Yanayi za ta fitar da tak**aiman jadawalin rarraba ruwa ga al’ummomi bayan kammala gwaje-gwajen tsarin da fara cikakken aiki.

20/09/2026

MACBAN: Gwamnatin Kano Ba Ta Saurari Buƙatun Fulani Yadda Ya Kamata Ba
Climate Watch Hausa (CWH)

Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana buƙatar ƙara samar da damarmaki ga al’ummar Fulbe, musamman wajen samun kuɗin jari, ilimi, kiwon dabbobi, ruwa, wuraren kiwo, kasuwanni da koyon sana’o’i.

Mataimakin Gwamnan Kano, Murtala Sule Garo, ne ya bayyana hakan yayin da yake wakiltar Gwamna Abba Kabir Yusuf a taron Tabital Pulaaku International Assembly da aka gudanar a Kano.

Gwamnatin ta kuma jaddada muhimmancin samar da ilimi ga yara daga al’ummomin makiyaya da karkara, da kuma ƙarfafa hanyoyin da za su inganta rayuwarsu da tattalin arzikinsu.

Sai dai a wani ɓangare na lamarin, ƙungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN) ta ce har yanzu akwai wasu muhimman buƙatun al’ummar Fulani da take ganin gwamnatin Jihar Kano ba ta saurare su yadda ya k**ata ba.

Shugaban MACBAN na Jihar Kano, Captain Abdullahi Adamu Bakoji (mai ritaya), ya bayyana hakan ne a wata zantawa ta musamman da Climate Watch Hausa (CWH).
Ya ce akwai buƙatar gwamnati ta ƙara sauraron ƙorafe-ƙorafen makiyaya da kuma ɗaukar matakan da za su taimaka wajen magance matsalolin da suke fuskanta, musamman waɗanda s**a shafi kiwo, wuraren kiwo, zaman lafiya da dangantakar manoma da makiyaya.
A gefe guda kuma, ana ci gaba da jaddada muhimmancin tattaunawa da fahimtar juna tsakanin manoma, makiyaya da sauran al’ummomi domin rage rikice-rikice da samar da zaman lafiya mai ɗorewa.

Me shugaban MACBAN na Kano ya ce game da yadda gwamnatin Kano ke kula da buƙatun Fulani?
🎥 Ku kalli cikakkiyar zantawar Captain Abdullahi Adamu Bakoji da Climate Watch Hausa (CWH) a bidiyon da ke ƙasa.

Climate Watch Hausa (CWH)
Kafar yada labarai da wayar da kai akan Sauyin Yanayi da inganta Muhalli

19/09/2026

SANARWAR MANEMA LABARAI — BIBIYAR LAMARI

MUTUWAR MUTANE 37 A HANNUN NSCDC: IHRC-RFT TA YABA WA IGP DISU, TA KUMA NEMI AYI CIKAKKEN BINCIKE MAI ZAMAN KANSA

19 Satumba 2026

Bayan sanarwar da IHRC-RFT Nigeria Chapter ta fitar dangane da mutuwar mutane 37 da ake cewa suna hannun Hukumar Tsaro da Kare Fararen Hula ta Najeriya (NSCDC), IHRC-RFT na yaba wa Sufeto-Janar na ’Yan Sandan Najeriya, IGP Olatunji Rilwan Disu, bisa gaggawar zuwa Jihar Neja domin ganawa da Gwamna Umaru Bago da kuma fara matakan bincike kan lamarin.

Zuwansa da kansa ya nuna cewa ya dauki wannan lamari da muhimmanci tare da fahimtar bukatar daukar matakin gaggawa.

IHRC-RFT ta kuma lura cewa Commandant-General na NSCDC yana Jihar Neja a yayin da ake tunkarar wannan lamari. Sai dai kasancewar jami’an da ke da alhakin kula da lamarin wani bangare ne na aikin da ya rataya a kansu, musamman idan aka yi la’akari da girman wannan lamari.

MUNA KIRA DA A YI CIKAKKEN BINCIKE MAI ZAMAN KANSA

IHRC-RFT na kira da a gudanar da cikakken bincike mai zaman kansa, gaskiya kuma a bayyane, domin gano ainihin abin da ya faru da kuma dalilan da s**a haddasa mutuwar waɗannan mutane 37.

Binciken ya k**ata ya duba rawar da Gwamnan Jihar Neja, Commandant-General na NSCDC, State Commandant, da duk sauran jami’ai da ma’aikatan da ke da alhakin tsarewa, kula da lafiyar waɗannan mutane da jin dadinsu s**a taka.

Ba mu yanke hukunci kan kowa ba. Abin da muke nema shi ne gaskiya, adalci, ɗaukar alhaki da cikakken bayani kan abin da ya faru, tare da daukar matakin da ya dace bisa sak**akon binciken.

Muna kuma kira da a tabbatar binciken ya kasance mai zaman kansa, ba tare da son rai ba, a bayyane kuma abin dogaro ga jama’a, musamman ta hanyar tabbatar da cewa waɗanda ayyukansu ko nauyin da ke kansu zai iya kasancewa cikin binciken ba su mallaki ko jagorantar binciken ba.

Idan bincike ya tabbatar da cewa an samu sakaci, gazawar aiki, cin zarafin iko ko karya doka a kowane mataki na alhaki, bai k**ata wani matsayi na gwamnati ya zama garkuwa daga ɗaukar matakin da doka ta tanada ba.

IHRC-RFT ZA TA CI GABA DA BIBIYA

Rayukan mutane 37 ba ƙaramin abu ba ne, kuma ba za mu bari a manta da wannan lamari ba.

IHRC-RFT Nigeria Chapter za ta ci gaba da bibiyar binciken, tattara bayanan da za a iya tabbatar da sahihancinsu, rubuta abubuwan da s**a faru da kuma gano duk wani abu da ke bukatar ƙarin bayani.

Za mu kuma aika rahotannin da s**a dace zuwa Hedikwatar IHRC-RFT da ke Geneva, Switzerland, bisa tsarin aikinmu da kuma hanyoyin da s**a dace na hulɗa da Majalisar Tattalin Arziki da Zamantakewa ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UN ECOSOC), wadda IHRC-RFT ke da Special Consultative Status.

Wannan ba barazana ba ce; wani bangare ne na nauyin da ya rataya a kanmu na kare da inganta haƙƙin bil’adama.

Muna sake yaba wa IGP Olatunji Rilwan Disu bisa gaggawar da ya yi da kuma shiga tsakani da kansa wajen wannan lamari.

Yanzu muna jiran gaskiya, adalci, ɗaukar alhaki da matakin da ya dace bisa sak**akon sahihin bincike mai zaman kansa.

BA ZA MU BAR RAYUKAN MUTANE 37 SU ZAMA ƘIDIDDIGA KAWAI A CIKIN RAHOTO BA.

SA HANNU:
Amb. Abdullahi Bakoji Adamu
Country Director, IHRC-RFT Nigeria Chapter
Security Analyst | Human Rights Advocate | Author
07034471678

18/09/2026

SANARWAR MANEMA LABARAI

IHRC-RFT TA YI KIRA DA GAGGAWAR BINCIKE MAI ZAMAN KANSA KAN MUTUWAR MASU HAƘAR ZINARIYA A JIHAR NEJA

18 Satumba 2026

Hukumar International Human Rights Commission – Relief Fund Trust (IHRC-RFT), Nigeria Chapter, ta bayyana matuƙar damuwa kan rahoton mutuwar mutane da dama bayan da jami’an Nigeria Security and Civil Defence Corps (NSCDC) s**a k**a wasu masu aikin haƙar zinariya tare da tsare su a wani wuri mai cunkoso.

Rahotanni sun nuna cewa an k**a mutanen ne bayan zargin cewa ana buƙatar biyan ₦150,000 kafin a ba da damar yin haƙar zinariya. Ana kuma zargin cewa an tsare su a wani ƙaramin wuri mai tsananin zafi da rashin isasshen iska, lamarin da ake danganta shi da mutuwar mutane da dama.

IHRC-RFT na kira ga Gwamnan Jihar Neja, Commandant-General na NSCDC, Ministan Harkokin Cikin Gida, Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai, NHRC, da sauran hukumomin da abin ya shafa da su gudanar da bincike mai zaman kansa, gaskiya da adalci, domin tabbatar da ainihin abin da ya faru da kuma ɗaukar matakin da ya dace idan an tabbatar da take haƙƙin ɗan Adam.

Mataki na 3 da na 5 na UDHR sun tabbatar da haƙƙin rayuwa da kariya daga azabtarwa ko mu’amala marar mutunci. Haka kuma, Sashe na 33 da 34 na Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya sun kare haƙƙin rayuwa da mutuncin ɗan Adam.

IHRC-RFT za ta ci gaba da bibiyar wannan lamari, tattara bayanai da neman adalci da ɗaukar alhaki har sai an tabbatar da gaskiyar abin da ya faru.

Amb. Abdullahi Bakoji Adamu
Country Director, IHRC-RFT Nigeria Chapter
Security Analyst | Human Rights Advocate | Author

17/09/2026

SANARWAR MANEMA LABARAI

IHRC-RFT TA YI KIRA DA A ƘARA WAYAR DA KAN JAMA’A DA RIGAKAFIN CUTAR MASHAKO (DIPHTHERIA)

Abuja, Najeriya — Satumba 2026

Ƙungiyar International Human Rights Commission – Relief Fund Trust (IHRC-RFT), Nigeria Chapter, na kira ga gwamnatoci, iyaye, makarantu, ma’aikatan lafiya, shugabannin gargajiya da na addini, da sauran al’ummomi a faɗin Najeriya da su ƙara himma wajen wayar da kan jama’a da ɗaukar matakan kariya daga cutar mashako Diphtheria, wadda cuta ce mai tsanani kuma mai iya yin sanadin mutuwa, amma ana iya kare mutum daga gare ta ta hanyar rigakafi.

Diphtheria na iya yaɗuwa ta hanyar numfashi yayin tari ko atishawa, ta hanyar kusanci kai tsaye da mai ɗauke da cutar, ko kuma ta wasu abubuwan da s**a gurɓata.

Alamomin farko na iya haɗawa da zazzabi, ciwon makogwaro, tari da majina. Idan cutar ta tsananta, tana iya haifar da wani abu mai kauri mai launin toka ko fari a cikin maƙogwaro, wahalar numfashi, kumburin wuya, da kuma matsaloli masu tsanani da za su iya shafar zuciya da jijiyoyin jiki.

DOLE MU KARE ’YA’YANMU

IHRC-RFT na matuƙar damuwa musamman game da yaran da ba su samu cikakkiyar rigakafin da ake buƙata ba.

Bisa ga ƙa’idodin NCDC, yara ya k**ata su samu allurai uku na rigakafin pentavalent a makonni 6, 10 da 14 bayan haihuwa. Yaran da s**a rasa wasu alluran rigakafi kuma za su iya amfana da shirye-shiryen cike gibin rigakafi (catch-up vaccination) da kuma shirye-shiryen rigakafin da ake yi lokacin barkewar cuta.

Saboda haka, muna kira ga kowane uba, uwa da mai kula da yara:

Ku duba halin rigakafin yaranku. Kada ku jira sai alamun cuta sun bayyana kafin ku ɗauki mataki.

Muna kuma kira ga gwamnatoci da hukumomin lafiya da su ƙarfafa shirye-shiryen rigakafi, sa ido kan cututtuka, wayar da kan jama’a, da kuma samar da damar samun ganowa da magani cikin gaggawa, musamman a ga mazauna karkara.

KADA A YI SAKACI DA ALAMOMIN TA

Duk wanda aka fahimci alamomin da ake zargin diphtheria ne, ya k**ata ya nemi kulawar lafiya nan take, sannan ya guji kusanci da wasu mutane ya kuma gaggauta neman shawarar ma’aikatan lafiya.

Mutanen da s**a yi kusanci da wanda aka tabbatar yana ɗauke da cutar ya k**ata a sa musu ido kuma a kula da su bisa ƙa’idojin kiwon lafiyar jama’a.

Haka kuma, ma’aikatan lafiya su tabbatar da cewa suna amfani da matakan kariya da hana yaɗuwar cuta yayin kula da waɗanda ake zargin suna da cutar.

KIRA GA DUKKAN ’YAN NAJERIYA

Diphtheria cuta ce da za a iya yin rigakafinta, kuma rigakafi na daga cikin hanyoyin da s**a fi tasiri wajen kare yara da al’umma.

Kada mu jira barkewar cuta kafin mu ɗauki mataki.

Iyaye su tabbatar da rigakafin ’ya’yansu.

Al’umma su yaɗa sahihan bayanai.

Makarantu su ƙara wayar da kan dalibai game da lafiya.

Gwamnatoci su ƙarfafa rigakafi da sa ido kan cututtuka.

Kuma kowane ɗan Najeriya ya ɗauki wannan gargaɗi da muhimmanci.

Hausawa kance Rigakafi ya fi magani.

KARE ’YA’YANMU.

YI RIGAKAFI.
ƊAUKI MATAKI DA WURI.
CETO RAYUKA.

Wanda ya fitar da sanarwar:

Amb. Abdullahi Bakoji Adamu
Country Director, IHRC-RFT Nigeria Chapter
Security Analyst & Human Rights Advocate
International Human Rights Commission – Relief Fund Trust (IHRC-RFT), Nigeria Chapter
Special Consultative Status with the United Nations Economic and Social Council (UN ECOSOC)

📞 07034471678

12/09/2026

SHIN ’YAN AREWA SUNA TSORON FADAR RA’AYINSU? 🗣️

Tsadar rayuwa, rashin aikin yi, matsalolin tsaro da sauran ƙalubale na ci gaba da damun jama’a.

Amma me ya sa wasu ke tsoron magana?

Shin lokaci ya yi da ’yan Arewa za su fito su bayyana abin da ke damunsu cikin lumana?

👉 Me ke damunka? Ka faɗi ra’ayinka cikin mutunci.

12/09/2026

🚨 DA DUMI-DUMI: RUNDUNAR SAKKWATO TA TABBATAR DA MUTUWAR MATASHIN DA YA HARI MALAM MUSA LUKUWA

Al-Manasik Reporters Hausa (AMR Hausa)

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Sakkwato ta tabbatar da mutuwar wani matashi da ya kai wa fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Musa Lukuman Lukuwa, hari a yankin Mabera.

A cewar rundunar, lamarin ya faru ne bayan kammala sallar Juma’a, inda matashin ya shiga Masallacin Lukuwa tare da kai wa Malam Musa Lukuwa hari da wuƙa.

Rahoton ya bayyana cewa matashin ya yanki Malam Musa Lukuwa a gefen wuyansa na hagu, kafin wasu mutane da ke wajen s**a far masa, inda ya rasa ransa kafin jami’an tsaro su isa wurin.

An kai gawar matashin zuwa asibiti, inda likita ya tabbatar da mutuwarsa.

Shi kuwa Malam Musa Lukuwa, an kai shi Asibitin Kwararru na Jihar Sakkwato domin samun kulawar likitoci, kuma daga bisani aka sallame shi zuwa gida.

Bayan faruwar lamarin, rundunar ta tura ƙarin jami’an tsaro zuwa yankin Mabera domin tabbatar da tsaro da dawo da doka da oda.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Sakkwato, Hayatu Hassan Shaffa, ya yi kira ga al’umma da su zauna lafiya, su guji ɗaukar doka a hannunsu, tare da ba jami’an tsaro haɗin kai wajen gudanar da bincike.

Rundunar ta kuma ce za ta gudanar da cikakken bincike kan lamarin tare da hukunta duk wanda aka samu da hannu wajen aikata laifi.

📌 AMR Hausa za ta ci gaba da kawo muku sahihan bayanai kan wannan lamari yayin da suke fitowa.

Al-Manasik Reporters Hausa (AMR Hausa)
📰 Sahihin labari cikin lokaci.

10/09/2026

Inna lillahi Wa Inna lillahi Raji'un

Allah Ya ya yi wa Alhaji Salisu Gaya, rasuwa a daren Alhamis 10 09 2026.
Kafin rasuwar marigayin ma'aikaci ne a Hukumar Alhazai Ta Nigeria NAHCON.

10/09/2026

ƘUNCIN RAYUWA YA ADDABI ’YAN AREWA

Tsadar kayan abinci, rashin aikin yi, ƙarancin kuɗin shiga da matsalolin tsaro na ci gaba da jefa al’ummar Arewacin Nigeria cikin damuwa.

Yayin da farashin kayan masarufi ke ƙaruwa, da dama daga cikin talakawa na fuskantar ƙalubalen ciyar da iyalansu, biyan kuɗin makaranta, kula da lafiya da sauran muhimman bukatun rayuwa.

Shin lokaci ya yi da ’yan Arewa za su fara magana a fili kan matsalolin da ke addabar su, tare da neman hanyoyin samun mafita?

💬 Me za ku ce? Ku bayyana ra’ayinku a cikin comments.

By Umar Ishaq Umar Sharada

09/09/2026

Shin ’Yan Arewa Sun San Gaskiyar Abin da Ke Damunsu, Ko Tsoron Yin Magana Ne Ke Hana Su?

Wannan na daga cikin tambayoyin da a yau ake ta muhawara a kansu.

Shin ’yan Arewa sun fahimci ainihin matsalolin da suke addabar al’ummarsu, amma tsoron abin da ka iya biyo baya ne ke hana su fito fili su bayyana ra’ayoyinsu?

Da dama daga cikin al’umma sun dade suna fuskantar matsalolin tsaro, tsadar rayuwa, rashin aikin yi, talauci da sauran kalubalen rayuwa.

Sai dai duk da haka, wasu mutane kan zabi yin shiru, ko dai saboda tsoron abin da zai iya faruwa idan s**a fito fili, ko kuma saboda wasu dalilai da s**a shafi siyasa, al’ada, zamantakewa da yadda al’umma ke kallon masu s**a.

A gefe guda kuma, akwai wadanda ke ganin cewa ba tsoro kadai ne dalilin yin shiru ba. Wasu na iya kasancewa ba su da cikakkiyar damar bayyana ra’ayinsu, yayin da wasu kuma suke ganin babu abin da zai canza ko da sun yi magana.

Masu sharhi kan al’amuran yau da kullum na ganin cewa, samun damar bayyana damuwa cikin lumana, mutunta juna da kuma neman mafita, na daga cikin hanyoyin da al’umma za su iya taimakawa wajen magance matsalolin da ke addabarsu.

To, mene ne ra’ayinka?

Shin tsoron magana ne ke hana ’yan Arewa neman sauyin da suke bukata, ko kuma akwai wasu dalilai da s**a fi haka?

Ku bayyana ra’ayoyinku cikin mutunci da lumana.

Want your public figure to be the top-listed Public Figure in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Address


Zawachiki
Kano
110001