Gwammaja Development Forum

Gwammaja Development Forum

Share

Gwammaja

09/09/2026

GDF TA KAI ZIYARA GA KWAMISHINAN BIBIYAR AYYUKA

A yau, Gwammaja Development Forum (GDF) ta kai ziyara ga Kwamishinan Bibiyar Ayyuka, Ƙididdigewa da Tabbatar da Ingancinsu, Comrade Nura Iro Ma’aji, domin bibiyar wasu muhimman ayyukan da s**a shafi al’ummar Gwammaja.

A yayin ziyarar, Shugaban GDF ya nemi ƙarin bayani kan halin da ake ciki game da aikin sabunta t**in Gwammaja–Mumbayya House zuwa Kofar Ruwa, da kuma samar da Ofishin Neighborhood na Ƙaramar Hukumar Dala.

A nasa jawabin, Kwamishinan ya bayyana cewa aikin t**in Gwammaja–Mumbayya House zuwa Kofar Ruwa yana cikin ayyukan da ake sa ran Maigirma Gwamnan Jihar Kano zai amince da su nan gaba kaɗan.

Game da Ofishin Neighborhood, ya bayyana cewa Gwamnatin Kano na son kammala ayyukan ƙananan hukumomin da ke wajen gari kafin ta koma cikin birnin Kano.

09/09/2026

SANARWAR FARA AIKIN GDF TRANSPORT

Gwammaja Development Forum (GDF) na farin cikin sanar da al’ummar Gwammaja fara aikin GDF TRANSPORT, wanda za a ƙaddamar da shi domin sauƙaƙa zirga-zirgar al’umma da samar da ingantaccen tsarin sufuri a cikin al’umma.

A ƙarƙashin wannan shiri, an samar da Adaidaita Sahu da za ta dinga ɗaukar fasinjoji daga bakin t**i zuwa cikin unguwar Gwammaja.

MUNA NEMAN:

🔹 Masu son tuƙin Adaidaita Sahu su shiga wannan shiri.

🔹 Masu son tallafa wa shirin ta hanyar samar da ƙarin Adaidaita Sahu domin faɗaɗa aikin da samar da ƙarin guraben ayyukan yi.

WURAREN TSAYAWA:

📍 Aljazeera Bus Stop
📍 Yan Kosai Bus Stop
📍 Ihya’ussunnah Bus Stop

Muna maraba da duk wanda yake son shiga cikin shirin ko bayar da gudunmawa domin wannan aikin ci gaban al’umma.

📞 Don ƙarin bayani:
07033043458 | 07088651691

Photos from Gwammaja Development Forum's post 07/09/2026

GDF TA MIƘA TAKARDU BIYU OFISHIN KWAMISHINAN AYYUKA

Gwammaja Development Forum (GDF) ta miƙa takardu biyu zuwa ofishin Kwamishinan Ayyuka domin neman ɗaukin gaggawa kan wasu muhimman matsalolin da s**a shafi al’ummar Gwammaja.

Takarda ta farko: Neman ɗaukin gaggawa kan ambaliyar ruwa da ke tasowa daga Kwanar Taya zuwa Kofar Ruwa, wanda ke shigowa cikin unguwar Gwammaja.

Takarda ta biyu: Neman sabunta t**in Gwammaja–Mumbayya House–Kofar Ruwa, bisa la’akari da irin lalacewar da t**in ya yi.

04/09/2026

SANARWA TA MUSAMMAN

SHIRIN SAMAR DA ILIMI GA YARAN GWAMMAJA

Gwammaja Development Forum (GDF), tare da haɗin gwiwa da UNICEF ABEP Learning Centres, na sanar da iyaye da masu kula da yara maza da mata Musamman marayu da marasa karfi daga Gwammaja cewa ana buƙatar yara masu shekaru 4 zuwa 15 waɗanda:
Ba sa zuwa makaranta.

Sun daina zuwa makaranta.

Iyayensu ko masu kula da su ba su da ikon ɗaukar nauyin karatunsu.

Ana kira ga iyaye ko masu kula da irin waɗannan yara da su zo gobe Asabar a Gidan Mai Unguwar Gwammaja dake kofar wakili domin samun cikakken bayani da yin rijista.

KO
Ku kira lambobin waya da ke ƙasa domin ƙarin bayani:
📞 07088651691
📞 07033804569

LOKACI: Gobe Asabar
WURI: Gidan Mai Unguwar Gwammaja

Wannan dama ce ga yaran Gwammaja maza da mata domin su samu damar komawa karatu.

26/08/2026

Ranar Hausa ta Duniya 🌍

A yau, 26 ga Agusta 2026, Gwammaja Development Forum (GDF) na taya al’ummar Hausa murnar Ranar Hausa ta Duniya.

Hausa ba harshe kaɗai ba ne; gadonmu ne, al’adarmu ce, kuma ginshiƙin haɗin kanmu ne.

Mu ci gaba da amfani da Hausa, koyar da ita, kare ta da bunƙasa ta.

GDF — Haɗin Kai da Ci Gaba.

25/08/2026

BARKA DA EID EL-MAULUD

A madadin Gwammaja Development Forum (GDF), muna taya daukacin al’ummar Musulmi a Najeriya da sauran sassan duniya, musamman al’ummar Gwammaja, murnar zagayowar Eid El-Maulud — ranar tunawa da zuwan fiyayyen halitta, shugaban Manzanni, Annabi Muhammad ﷺ.

Wannan ba lokaci ne na murna kawai ba; lokaci ne na sabunta ƙauna, tunawa da koyarwa da kuma yin koyi da kyawawan halayen Manzon Allah ﷺ — gaskiya, amana, adalci, tausayi, haƙuri da kishin al’umma.

A cikin koyarwar Manzon Allah ﷺ akwai babban darasi game da shugabanci da amana. Ya koya mana cewa wanda aka ɗora wa nauyin al’umma ba mai mulki kawai ba ne, mai kula da amana ne, kuma zai kasance abin tambaya a gaban Allah.

Saboda haka, yayin da muke tunkarar zaɓe mai zuwa, ya kamata mu tuna cewa ƙuri’a amana ce.

Kada mu bari ɗan abin da za a ba mu na ɗan lokaci ya sa mu sayar da makomar al’ummarmu.

Mu zaɓi shugabanni bisa amana, gaskiya, adalci, cancanta da kishin jama’a. Mu tantance ayyuka da halaye, ba hayaniya da alkawuran lokacin yaƙin neman zaɓe kawai ba.

🤲 Allah Ya sanya mu cikin waɗanda suke ƙaunar Manzon Allah ﷺ da gaske, suna bin koyarwarsa, suna riƙe da amana, suna yin adalci, kuma suna amfani da duk wata dama wajen kawo ci gaba ga al’umma.

Allah Ya albarkaci al’ummar Musulmi, musamman al’ummar Gwammaja. Ya kawo mana shugabanni nagari, Ya tabbatar da zaman lafiya da haɗin kai a Najeriya.

🌙💚 EID EL-MAULUD MUBARAK!

Gwammaja Development Forum (GDF)
Unity And Progress

13/08/2026

GDF NA TAYA MURNA!

Kungiyar Gwammaja Development Forum (GDF) na taya ɗaya daga cikin iyayenta, Prof. Bilkisu Dahiru Gwammaja, murnar zama cikakkiyar Farfesa a fannin Larabci a Jami’ar Bayero, Kano.
Wannan babban ci gaba ne da ya cancanci alfahari. Muna yi mata fatan ƙarin nasara, hikima, lafiya da albarka wajen ci gaba da hidimtawa ilimi da al’umma.

Daga:
Dukkan ’yan Gwammaja Development Forum (GDF)

10/08/2026

SHUGABANNIN GDF SUN SAMU HORO NA MUSAMMAN

Shugabannin Gwammaja Development Forum (GDF) sun samu horo na musamman daga Nura Ahmad Muhammad Esq., Shugaban Mufarka Youth Development Initiative.
Horarwar ta mayar da hankali kan hanyoyin tafiyar da ƙungiya, ƙwarewar shugabanci, tsara manufofi da kuma yadda za a inganta tasirin ƙungiya a cikin al’umma.

GDF na godiya da wannan muhimmiyar gudummawa, tare da fatan ilimin da aka samu zai taimaka wajen ƙara inganta ayyukan ƙungiyar da hidimarta ga al’ummar Gwammaja.

07/08/2026

AN KAMMALA SHIRIN DUBA IDO DA BA DA GILASHI KYAUTA A GWAMMAJA

Alhamdulillah, an kammala shirin Duba Ido da Ba da Gilashi Kyauta a Gwammaja, wanda ya gudana tsawon kwanaki 5.

A yayin shirin, an duba marasa lafiya tare da ba da gilashi sama da 700 kyauta, domin taimakawa al’umma wajen inganta lafiyar idanu da gani.

A ranar ƙarshe, Gwammaja Development Forum (GDF) tare da Gwammaja Media Connect sun mika takardar yabo ga ƙungiyar Seewell and Care Consult, wadda ta jagoranci ƙwararrun likitocin da s**a gudanar da wannan aikin alheri.

GDF & Gwammaja Media Connect na godiya ga Seewell and Care Consult da duk waɗanda s**a bayar da gudummawa wajen ganin wannan shiri ya yi nasara.

05/08/2026

DUBA IDO DA BA DA GILASHI KYAUTA A GWAMMAJA

Alhamdulillah! Zuwa rana ta biyu na shirin Duba Ido da Ba da Gilashi Kyauta a Gwammaja, fiye da mutum 300 sun rabauta da wannan tallafin lafiya.
Shirin zai ci gaba har na kwana shida, domin bai wa ƙarin al'umma damar cin gajiyarsa.

GDF × Gwammaja Media Connect × Seewell and Care Consult

Want your organization to be the top-listed Non Profit Organization in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Website

Address


Kofar Wakili Gwammaja Special Primary School
Kano

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Gwammaja Development Forum posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Subscribe

We will notify you when anything happens in Kano.