N R HAUSA TV
Wannan shafi ne da zai ke kawo muku labarai ingantattu waɗanda babu wai-wai. WhatsApp Number 08139283352.
01/07/2025
Shout out to my newest followers! Excited to have you onboard! Senatorr Usman Forlife, Abdurrahim Umar Kura, B M Abdullahi Maitaya, Ameenerh Abdullah Ameenerh Abdullah
29/06/2025
An kaddamar da shugabancin ƙungiyar Minjibir/Ungogo Kwankwasiyya concern forum.
Kungiyar dai ta tsaida matsaya kan tabbatar da shugabanci na gari a Minjibir da Ungogo da kuma kawar da baragurbin shugabanni a yankin.
A zaman ƙungiyar na farko a zaɓi shugabancin rikon kwarya inda Abubakar Bachirawa ya kasance shugaban kungiyar.
Abba Kabir Yusuf
Hon. Sani Wakili
Kwankwasiyya Reporters
Rahama Sadau
29/06/2025
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da Sakataren Jam’iyyar na Kasa, Mista Oginni Olaposi, ya fitar ranar Lahadi a Legas.
Olaposi ya mayar da martani ne kan murabus din da Abdullahi Ganduje ya yi daga shugabancin APC da kuma jita-jitar cewa ya yi hakan ne domin ba wa Kwankwaso damar shiga jam’iyyar.
“Kwankwaso ya ci amanar da muka ba shi ta hanyar kokarin kwace jam’iyyar daga hannun wanda ya kafa ta, Dokta Boniface Aniebonam, wanda ya ba shi damar samun tikitin takarar shugaban kasa kyauta a 2023,” in ji shi.
28/06/2025
Har yanzu al'ummar Gayawa Titin Badaru dake yankin karamar hukumar Ungogo na fama da matsalar zai-zayar ƙasa.
Abba Kabir Yusuf
Gandujiyya Online
Aminu Saira
Rahama Sadau
28/06/2025
Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana cewa babu wani sauyi da aka samu a matsayin Sanata George Akume, wanda har yanzu ke ci gaba da zama Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF).
Wannan na zuwa ne bayan yaduwar jita-jita da ke cewa an sauke shi daga mukaminsa.
A cewar wata sanarwa da Bayo Onanuga, mai ba Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu shawara na musamman kan harkokin yada labarai ya fitar a yau Asabar, Shugaban Ƙasa bai yi wani sabon naɗi ba dangane da mukamin SGF.
Abba Kabir Yusuf
Rahama Sadau
Aminu Saira
Gandujiyya Online
28/06/2025
Mai dakin shugaban kasa Mr. Remi Bola Ahmad Tinubu ta bada tallafin Naira miliyan 110 ga iyalan yan wasan jihar Kano 22 wadanda s**a rasu sakamakon hatsarin a hanyarsu ta dawowa gida bayan kammala gasar wasannin motsa jiki ta kasa.
Da take gabatar da tallafin ga iyalan mamatan, Mai dakin shugaban kasa Mrs. Remi Tinubu wadda ta samu wakilcin Mai dakin mataimakin shugaban majalisar dattijai Hajiya Laila Barau Jibril, ta bayyana alhininsa bisa rasuwar su.
28/06/2025
Waiwaye: ko me ƴan Nigeria zasu iya tunawa a wannan ranar?
28/06/2025
Ana neman tono gawar tsohon Gwamnan Jihar Oyo, Otunba Christopher Adebayo Alao-Akala, domin yin gwajin jini (DNA) da nufin tantance halastattun ’ya’yansa da za su ci gadon dukiyar da ya bari.
Me zaku ce?
28/06/2025
An shiga ruɗani bayan sace wata mashahuriyar Tukunya da ta kai kimanin shekaru 30 ana girki da ita.
Matashi Abdurrahim Umar Kura shi ne ya wallafa ɓacewar Tukunyar wanda ya ce sun girgiza da jin sace wannan Tukunya la'akari da yadda ɗanɗanan girkin ta daban yake da sauran Tukwane.
Zalika matasin ya bukaci duk wanda yaga wannan Tukunya tasu da ya taimaka ya tuntube su.
28/06/2025
Fagen wasanni: A irin wannan ranr ta 28-06-2007 ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcalona ta ɗauki ɗan wasa Yaya Touré akan kuɗi €9M.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Address
Kano