YALWA Development FORUM YDF

YALWA Development FORUM YDF

Share

Gamayyar kungiyoyin sa kai na Yalwa dake aiki a dunkule domin kawo cigaba da zaman lafiya mai dorewa

08/09/2026

Mun samu bishiyoyi guda 600 domin dasawa afadin Yalwa da kewaye. Masu bukata suyi magana.

07/09/2026

Assalamu alaikum,

Ina amfani da wannan damar wajen sanar da samuwar bishiyu da mukayi a mazabar Yalwa,G/dutse karamar hukumar Dala, a ƙarƙashin shirin gwamnatin jihar Kano na yaƙi da dumamar yanayi da kwararar hamada a cikin jihar Kano da kewaye, da haka nake shaidawa al'ummar wannan yankin a kowane layi ko lungu matukar kuna da bukatar bishiya ka tuntube ni ta nan sahar ko kuma kayi min Magana ta What's app.
Muna masu rokon al'umma duk wanda ya karbi bishiya don Allah ya bata kulawa ta musamman don samun abun da ake buƙata.

07060811212/07068956659

🌴🌴🌴🌴🌿🌿🌿🌿☘️☘️☘️🪴🪴🪴🌳🌳🌳🌳🌳

04/09/2026

SANARWA
Akwai likitocin idanu da zasu zo makarantar Anwaru gobe Asabar da Lahadi domin duba masu matsala ta ido tare da basu glass kyauta . Zaa fara da misalin karfe 8:30 na safe.

03/09/2026

Munsamu allocation na bishiyoyi amma debowa ya gagaremu saboda nursery din a Gwarzo yake...

Photos from YALWA Development FORUM YDF's post 05/08/2026

A yau Laraba 5 ga watan Agusta 2026 mai girma zababben shugaban karamar hukumar Dala ya jagoranci bikin bude ofishin civil defence a Yalwa domin inganta tsaro a fadin yankin.

02/08/2026

Insha Allah nan bada jimawa ba gamayyar kungiyoyin Yalwa hadin gwiwa da zasu qaddamar da dashen biyoyi a fadin Yalwa da kewaye domin samun ingantaccen yanayi afadin yankin.

Photos from YALWA Development FORUM YDF's post 23/06/2026

Halin da makarantar Anwaru special primary school ke ciki kenan tsawon watanni 😢.

Muna kira ga mahukunta da masu kishin ilimi na yankin da su yiwa Allah su dubi halin da wajen yake ciki da kuma halin da daliban suke.

21/04/2026

Shout out to my newest followers! Excited to have you onboard! Idris Ishaq Abdulkarim, Ayuba Sunusi, Sulaiman Mukutar

09/02/2026

Jawabin Malam Lawan yayin yaye daliban .

Photos from YALWA Development FORUM YDF's post 08/02/2026

KWARYA KWARYAR BIKIN YAYE DALIBAI

A yau Lahadi 8 ga watan February makarantar koyon sana'o'i dake Yalwa Model vocational center tayi bikin yaye dalibai wadanda s**a samu horo na musamman na koyon sana'o'i tun bayan dawowar center aiki .

Wadannan dalibai sun koyi sana'o'i da s**a hada da :

Dinki na mata
Leather works ( Hada takalmi da jaka )
Aikin stone na mayafai
Da general courses.

Taron ya samu halartar masu unguwannin Yalwa da Gorondutse da kansilan Yalwa a inda Hon. Councilor ya bada gudunmawar naira dubu hamsin ( N50 000 ).

Muna adduar Allah ya kara shiga lamarin wannan unguwa dama Dala baki daya ya kara karfafar kwamati na Yalwa Development forum .

Want your organization to be the top-listed Non Profit Organization in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Website

Address


Yalwa Dala Local Government
Kano