Solacebase Hausa
Shafin jaridar SolaceBase Hausa
12/08/2026
Matashi ya mutu bayan ya fada kududdufi a jihar Kano
Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta sanar da cewa wani matashi mai shekaru 18, Abdullahi Aminu, ya nutse tare da rasa ransa bayan ya fada wani kududdufi a Kofar Gabas da ke Karamar Hukumar Danbatta a Jihar Kano.
Duba labari a kasa:
12/08/2026
Zaben Osun: Rundunar ‘Yan Sanda ta gayyaci Sanata kan kalaman barazanar kisa a wani bidiyo dake yawo
Rundunar ‘yan sandan jihar Osun ta gayyaci dan majalisar dattawa mai wakiltar mazabar Osun ta Gabas, Sanata Francis Fadahunsi, kan zargin barazanar da ya yi wa mambobin jam’iyyar AP gabanin zaben gwamnan jihar da za a yi a ranar Asabar.
Duba labari a kasa:
12/08/2026
Babu daga kafa a yakin da ake yi da miyagun kwayoyi a Kano – Muhuyi
Shugaban Hukumar Hadin Gwiwa ta Jihar Kano kan Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi, Alhaji Muhuyi Magaji Rimin Gado, ya bayyana cewa ba za a kyale kowa ba a yakin da ake yi da shaye-shaye da fataucin miyagun kwayoyi a jihar, inda ya yi gargadin cewa duk wanda aka k**a da hannu a wannan haramtacciyar sana’a zai fuskanci cikakken fushin doka.
Duba labari a kasa:
12/08/2026
Babu wata kungiyar addini da ya k**ata ta dauki kanta madaukakiya fiyye da wata – Sultan
Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar III, ya yi kira ga Kiristoci da Musulmi a Najeriya da su daina zagin juna, inda ya bayyana cewa hakuri da juna tsakanin mabiya addinai daban-daban yana da muhimmanci domin zaman lafiya.
Duba labari a kasa:
11/08/2026
Shugaban karamar hukumar Kabo ya kori Sakataren Mulki da wasu mutum 4
Shugaban Karamar Hukumar Kabo ta Jihar Kano, Lawan Najume Kabo, ya kore Sakataren mulki tare da wasu masu rike da muk**an siyasa guda hudu bisa zargin kasancewarsu mambobin kungiyar goyon bayan Tinubu Maliya Shonikan (TMS) a Jihar Kano.
Duba labari a kasa:
11/08/2026
Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya ta bude aikin fara daukar ma’aikatan Short Service
Rundunar Sojin Ƙasa ta Najeriya ta bude dandali don neman aikin soja na musamman wato Short Service Combatant Commission Course 50/2027 ga ‘yan Najeriya da s**a cancanta, cikin har da fararen hula da kuma jami’an da ke aiki a halin yanzu.
Duba labari a kasa:
11/08/2026
Al’ummar Jigawa sun kaddamar da shirin taimakon gaggawa na kiwon lafiya
Mazauna al’ummar Rorau da ke Karamar Hukumar Kazaure a Jihar Jigawa sun kaddamar da tsarin adana kudi na jama’a domin taimakawa gidaje wajen biyan kudin maganin gaggawa da kuma rage jinkirin neman magani.
Duba labari a kasa:
10/08/2026
FUD ta bayyana dalilin sallamar malamar jami’ar
Jami’ar Tarayya ta Dutse (FUD) da ke Jihar Jigawa, ta musanta zargin keta hakkiin daukar ma’aikata, bata suna da kuma hana damar kare kai da tsohuwar malamar jami’ar, Dr. Ramla Muhammad Kamal, ta yi biyo bayan korar ta da aka yi daga aiki.
Duba labari a kasa:
10/08/2026
A kafa Tinubu yake tafiya zuwa ofis, sau daya kacal kuma yake cin abinci a rana – Zacch Adedeji
Shugaban Hukumar Kudaden Shiga ta Kasa (NRS), Zacch Adedeji, ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu yana takawa da kafa zuwa ofishinsa kuma sau daya kacal yake cin abinci a rana, inda ya musanta zargin cewa shugaban na gudanar da rayuwar almubazzaranci.
Duba labari a kasa:
10/08/2026
Hukumar Kiyaye Hadura ta tabbatar da mutuwar mutum 15, yayin da 25 s**a jikkata a hatsarin mota a Neja
Kwamandan Hukumar Kula da Kare Haddura ta Kasa (FRSC) a Jihar Neja, Aishatu Sa’adu, ta tabbatar da mutuwar matafiya 15, yayin da aka garzaya da wasu 25 zuwa asibiti biyo bayan wani mummunan hatsarin mota da ya auku a kan titin Enagi zuwa Mokwa.
Duba labari a kasa:
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the business
Telephone
Website
Address
Murtala Muhammad Way
Kano
234001