Ad One Zee Rk

Ad One Zee Rk

Share

KANAWA FILM PRODUCTION KANO

20/09/2026

HAJIYA SAFARA'U ZEENARIYAR PANTAMI TACE MALAM ZAIYI MULKI BISA ADALCI...
Rubutawa: Abdussamad Tijani Sani ...✍️

A yayin da ake ci gaba da shirye-shiryen tunkarar babban zaben Gwamnan Jihar Gombe na 2027, batun yadda za'a samar da shugabanci mai adalci, tausayi da kuma haɗin kan al’umma na daga cikin muhimman batutuwan da ke jan hankalin jama’a.

Hajiya Safara’u Zeenariyar Pantami ta bayyana cewa babu shakka, idan Allah Ya ba Professor Isa Ali Pantami damar jagorantar Jihar Gombe, mulkinsa zai kasance bisa adalci, daidaito da kuma kula kyautatawa da kowa, ba tare da la’akari da addini ko bambancin al’umma dana kabila ba.

A cewar Hajiya Safara’u, daga cikin fahimtar Isa Ali Pantami, ya fahimci cewa shugabanci shine ayi wa al’umma hidima, domin gwamnati ba ta wani bangare ko wata ƙungiya ba ce, sai dai amanar da aka ba shugaba domin ya kula da muradun jama’a baki ɗaya, wanan dalili yasa al'ummar Gombe baki daya suke lale da marhaban da ganin nasarar malam.

Ta ce Musulmai da Kiristoci, maza da mata, matasa da manya, kowa zai samu damar amfana da tsarin adalcin shugabancin malam cikin mutunci da adalci, ba tare da nuna wariya ko fifita wani saboda addini ba, ko kabila ba.

Wannan ra’ayi ya yi daidai da abin da Pantami ya bayyana a lokacin da ya samu tikitin PDP na Gombe, inda ya yi alkawarin gudanar da mulki bisa fairness, justice and accountability idan aka zaɓe shi.

Daga ƙarshe, Hajiya Safara’u ta jaddada cewa adalci shi ne ginshiƙin zaman lafiya, kuma shugabancin da ya haɗa kowa zai taimaka wajen ƙarfafa haɗin kan al’ummar Gombe, kuma lallau Gombe tana buƙatar shugabancin malam da zai ɗauki kowa a matsayin ɗan jiha ɗaya ba tare da wariya ba.

Prof. Isa Ali Pantami National Supporters Forum

Prof. Isa Ali Pantami Media & Digital Movement Abba Sani Pantami

Asmau Gambo
Hajiya Innayo Isah
Nana Dayyab
Facebook

Adam M Sadeeq

Ad One Zee Rk

19/09/2026

A SHEKARAR FARKON MULKIN MALAM…
Rubutawa: Abdussamad Tijani Sani....✍️

Hajiya Aisha wato Nana Dayyab, Wakiliyar First Lady, ta bayyana cewa idan Allah Ya ba Malam Professor Isa Ali Pantami nasara a zaɓen Gwamnan Jihar Gombe na 2027, al’ummar jihar za su fara ganin sauyin gwamnati tun daga shekarar farko.

A cewar Hajiya Aisha Dayyab, gwamnatin da Malam Isa Ali Pantami zai kafa za ta zo ne da sabon salo na shugabanci, tsari da kuma mayar da hankali kan abubuwan da s**a shafi rayuwar al’ummar Jihar Gombe kai tsaye.

Ta ce: “Idan Allah Ya ba Malam Isa Ali Pantami nasara a zaɓen 2027, muna masu tabbatar muku cewa a shekarar farko, Jihar Gombe da al’ummar jihar baki ɗaya za su gane cewa an samu sauyin gwamnati.”

Wannan magana ta zo ne a daidai lokacin da ake ƙara samun tattaunawa kan makomar siyasar Jihar Gombe da irin shugabancin da al’umma ke fata a shekarar 2027.

A cewar Hajiya Aisha Dayyab, abin da ake magana a kai ba wai sauyin suna ko sauyin mukami kawai ba ne, sai dai sauyin tsarin aiki da kuma yadda gwamnati za ta mayar da hankali wajen hidimtawa al’umma.

2027 na ƙara kusantowa, kuma lokaci ne da al’umma za su saurari manufofi, su tantance alkawura, sannan su yanke shawarar wanda za su bai wa amanar shugabancinSu.
Gombe Ta Malam Ce, Allah Ya Bamu Nasara.

Prof. Isa Ali Pantami National Supporters Forum
Abba Sani Pantami
Professor Isa Ali Pantami
Zeenariyar Pantami
Asmau Gambo
Oga Ameer Presdo
Facebook

Adam M Sadeeq
Nana Dayyab
Ad One Zee Rk

13/09/2026

DARAJAR MANZON ALLAH TA WUCE YADDA MUKE TSAMMANI...

Hakika sanin kowa ne, Manzon Allah yana da daraja da matsayi da babu wanda ya san cikakken girmansa da hakikanin martabarsa sai Allah Maɗaukakin Sarki.

Manzon Allah shi ne mafificin halitta wajen alheri, kamala, ɗaukaka, daraja, martaba da kyawawan halaye. Saboda haka, a kwatanta shi da wani mutum, ko da kuwa wannan mutumin yana da girma da daraja a idon mutane, ba daidai bane, domin babu wanda ya kai matsayin Manzon Allah, b***e ayi misali dashi ta ko wacce siga.

Mu fahimci wannan sosai: kwatanta Manzon Allah da wani mutum, ko da kuwa da niyyar yabo ne, ko hankaltar da mutane akan wani sako, to tauye girman matsayin Manzon Allah ne, domin matsayinsa ya fi duk abin da tunaninmu zai iya kaiwa, kuma ya wuce ayi misali dashi da kowa ta ko wacce siga.

Ya zama wajibi mu kiyaye harshenmu da maganganunmu idan muna magana game da Manzon Allah, ya zama dole mu koyi ladabi, girmamawa da tsananin kulawa da duk abin da ya shafi Manzon Allah, kada mu bari mi zake har kalmomin da muke amfani dasu su rage girman da ya dace da shi, ko mu yi amfani da wani mutum a matsayin ma'aunin kwatanta shi.

Manzon Allah shi ne mafificin halitta. Matansa sun fi matan kowa daraja, iyayensa sunfi iyayen kowa, domin suna da matsayi na musamman a wajen Allah, gidansa ya fi kowane gida daraja, zuriyarsa tana da matsayin da ta wuce ko wacce zuriyya daukaka, rayuwarsa ita ce mafi ɗaukaka, darajarsa ta fi darajar kowa, martabarsa ta fi martabar kowa, kuma ɗaukakarsa ba ta misaltuwa, b***e a misalta shi da wani kaskantacce.

Haka nan, duk abin da ya kasance na musamman a gare shi yana da nasa matsayi da girmamawa, dabbobinSa sunfi ko wacce dabba alheri, takalmi, riga, rawani, da duk abin da yake na shi ne yafi na kowa daukaka da daraja, Don haka, idan har muna ikirarin ƙaunar Manzon Allah, to ƙaunar ya kamata ne ta bayyana ne cikin ladabi, girmamawa, kiyaye harshe da kiyaye martabarsa.

Ba komai ba ne ya kamata mu mayar da shi abin kwatance, ba kowane irin yabo ne da kirari ya dace a yi wa Manzon Allah shi ba, Akwai kalmomin da zamu iya yabon wani mutum dasu, akwai kalmomin da zamu iya kirari wa wani mutum dasu, amma Manzon Allah ya wuce muyi amfani da wayan nan kalmomin gareShi saboda darajarSa ta wuce haka, domin Manzon Allah ba mutum ne da za a ɗora shi a kan ma'aunin sauran mutane ba. Shi ne Mafi Alherin Halitta, Mafi Kyawun Halaye, kuma Mafificin Manzannin Allah kwata.

Saboda haka, mu gayawa kanmu gaskiya, mu gyara kalmominmu, mu ƙara ladabi, mu ƙara girmamawa, mu kuma kiyaye duk abin da ya shafi Manzon Allah. Duk wanda yake son Manzon Allah, dole ne ya girmama shi, duk wanda yake girmama shi, dole ya kiyaye harshensa a kansa, kuma duk wanda ya san darajarsa, ba zai yi gaggawa da karambanin kwatanta shi da kowa ba.

Allah Mun tuba ka yafe mana, Allahumma salli wa sallim wa barik ala Sayyidina Muhammad.

Professor Isa Ali Pantami
Abba Sani Pantami
Nana Dayyab
Adam M Sadeeq
Abdussamad Tijani Sani

Ad One Zee Rk ....✍️

11/09/2026

YAUMIL JUMA’A...

A madadin Ofishin First Lady, Hajiya Khadija Professor Isa Ali Pantami, da dukkan da jagororin wanan office da ma’aikatan da ke ƙarƙashin wannan ofishi, na miƙa saƙon barka da Juma’a ga ’yan uwa Musulmi baki ɗaya, tare da addu’ar Allah Ya sanya wannan rana ta kasance mana rana mafi alkhairi, mafi dacewa da rahama da albarka.

Juma’a rana ce mai girma, rana ce ta tunatarwa da, ibada da neman kusanci da Allah. Don haka, wannan ofishi yana ƙara tunatar da mu muhimmanci da falalar yawaita salatin Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wassalam, dagewa da addu’a, istigfari da kyawawan ayyuka a wannan rana mai albarka. Allah Ya ce: Lallai Allah da Mala’ikunsa suna yin salati ga Annabi. Ya ku waɗanda s**a yi imani, ku yi salati a gare shi, da sallama. Don haka a kara himma a wanan rana.

Allah Ya karɓi ibadunmu, Ya gafarta mana zunubanmu, Ya biya mana buƙatunmu na alkhairi, Ya sanya albarka cikin rayukanmu da iyalanmu, Ya ba mu zaman lafiya da kwanciyar hankali. Allah Ya maimaita mana Juma’o’i cikin imani, lafiya, arziki da rahama, Ya Rabbal Alamin.

Wanan sako ne daga Office First Lady Hajiya Khadija Isah Ali Pantami....

Nana Dayyab
Zeenariyar Pantami
Asmau Gambo
Abba Sani Pantami
Prof. Isa Ali Pantami National Supporters Forum Professor Isa Ali Pantami

06/09/2026

MU ZAMA MASU KOYI DA RAYUWAR MANZON ALLAH...

Rayuwar Manzon Allah ba tarihi ba ce kawai da ake karantawa a wuce ba, rayuwa ce da ta kamata mu dauka a matsayin abin koyi da jagorantar dukkan al’amuran rayuwarmu. Idan muna son zaman lafiya, mu koyi yadda Annabi ya kasance mai tausayi da yafiya. Idan muna son adalci, mu koyi yadda ya kasance mai adalci ga kowa, idan muna son samun nasara, muyi koyi da hakurinsa, juriyarsa da dogaro da Allah a lokacin jarabawa.

Haka kuma, idan sabani ko rashin fahimta ya taso tsakaninmu, kada mu bari ya zama sanadin kiyayya, rarrabuwa ko gaba ko cin zarafin juna. Mu koma ga hanyoyin da Manzon Allah ya tsara mana, mu saurari juna, mu yi magana cikin hikima da ladabi, mu guji zagi da cin mutunci, mu yafe wa juna, sannan mu nemi sulhu da sasanci idan bukatar hakan ta taso.

Domin Manzon Allah ya koya mana cewa karfin al’umma ba ya cikin yawan rigima, sai dai cikin haɗin kai, haƙuri, adalci, yafiya da kyakkyawar mu’amala. Saboda haka, kada soyayyarmu ga Manzon Allah ta tsaya ga furta kalmomi kawai. Mu nuna wannan soyayya ta hanyar bin Sunnarsa a zahiri, a cikin gidajenmu, mu’amalarmu, shugabancimmu, kasuwancinmu, abokantakarmu da kuma yadda muke magance sabani.

Mu zama masu koyi da rayuwar Manzon Allah a ko yaushe, domin shi ne mafi kyawun abin koyi a gare mu. Allah Ya sanya mu cikin wadanda suke son ManzonSa da gaske, Ya ba mu ikon bin Sunnarsa, Ya kyautata halayenmu, Ya hada zukatanmu a kan gaskiya da alheri, Ya kuma hada mu da cetonSa.

Ad One Zee Rk.....✍️

04/09/2026

CEWA KU YI UMARNI DA MAI KYAU, KU YI HANI GA MUMMUNA…
Wanan ba ra'ayi bane, ba ganin dama bane, dole ne...

Idan muka koma cikin tarihi, musamman tarihin Annabi Musa (A.S.), za mu fahimci cewa Allah yana ɗaukaka waɗanda s**a tsaya kan gaskiya, s**a yi umarni da alheri, s**a kuma yi hani da mummuna.

Annabi Musa (A.S.) bai mallaki ƙarfin mulki, dukiya da yawan mabiya da Fir’auna yake da su ba. Fir’auna yana da iko, yana da dukiya, yana da runduna, kuma yana da tsarin mulki mai ƙarfi. Amma duk da wannan, Allah ya ba Annabi Musa (A.S.) nasara a kan Fir’auna.

Mun taba tambayar me ya sa? Saboda Musa (A.S.) ya tsaya kan abin da Allah ya umurce shi da shi. Bai sayar da gaskiya saboda tsoron iko ba, bai ɓoye gaskiya saboda neman wata duniya ba, kuma bai bar abin da ya yi imani da shi saboda son zuciya ba. Wannan darasi ne mai kyau da ya kamata mu gane mu kuma koya.

Me zai sa mu ji tsoron yin umarni da alheri saboda muna neman wani matsayi? Me zai sa mu ga abin da bai dace ba, amma mu yi shiru saboda muna neman wani abu? Me zai sa mu ga barna, amma mu kasa cewa wannan ba daidai ba ne, saboda muna tsoron kada a ce mun ɓata wa wani rai? Shin ba Allah ne yake bayar da komai ba? Shin don muna neman goyon bayan mutane sai mu manta da umarnin Allah?

Kar mu manta cewa Allah ne Mai bayar da nasara, Shine Mai ɗaukaka wanda Ya so. Allah ne Mai sauya yanayi, kenan idan mun yi imani cewa Allah ne yake ba da nasara, me zai sa mu cire umarninsa daga cikin al'amuranmu saboda son zuciya ko neman yardar mutane?

A siyasa, a kasuwanci, a shugabanci da kuma rayuwa gaba ɗaya, babu inda aka cire maka umarni da alkairi da hani ga sharri, babu wata hujja a sharia idan kuma akwai a kawo.

Hana mummuna ba yana nufin ƙiyayya ga wasu mutane ba ne, nasiha ce domin gyara, kuma Allah ne yace mu isar da nasiha a duk inda muka kasance, kada neman duniya ya sa mu rasa lahira, kada neman matsayi ya sa mu sayar da ƙa'idarmu, kada neman goyon bayan mutane ya sa mu manta da Ubangijin dake bayar da nasara.

Domin duk wanda ya dogara ga Allah, ya tsaya kan gaskiya, ya yi abin da ya dace, to ba ya rasa komai ko da mutane sun juya masa baya, kuma wallahi shine da nasara..

Allah Ya sa mu kasance cikin masu umarni da alheri, masu hani da mummuna, masu gaskiya da adalci, duk lamarin da babu umarni ga Alkairi Allah ka raba mu dashi, ko da acikin gidanMu da dakinmu yake.

Ad One Zee Rk ....✍️
Adam M Sadeeq
Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa
ELsuraj Muhammad Adam
Sheikh Ibrahim Saleh الشيخ ابراهيم صالح الحسيني
Professor Isa Ali Pantami

Want your public figure to be the top-listed Public Figure in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Website

Address


Kano