ISAH Muhammad ADAM
من خص وخص
01/08/2026
Malamin addinin Musulunci Imam Ahmad Junaidu ya bayyana haka a shafinsa na Facebook.
Hakan na zuwa ne bayan fitar wata waƙa da mawakin siyasa Dauda Kahutu Rarara yayi, wacce ake alaƙanta ta da zambo ga Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, ɗan takarar gwamnan jihar Gombe a jam'iyyar PDP.
01/08/2026
Gombawa Insha Allah Malam Isa Ali Ibrahim Pantami nakune kuma kunashinee
professor muna maka fatan alheri
01/08/2026
Gwamnatin Tarayya Ta Musanta Shirin Ƙara Kuɗin Wutar Lantarki; Ta Ce Inganta Hidima Ne A Gaba
Ministan Wutar Lantarki, Joseph Tegbe, ya bayyana cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba ta da wata manufa ta ƙara kuɗin wutar lantarki fiye da yadda yake a halin yanzu.
Ya ce abin da gwamnati ta fi mayar da hankali a kai ba ƙara kuɗin lantarki ba ne, sai dai inganta samar da wuta, tabbatar da kowa ya samu na'urar auna amfani da wuta (meter), da kuma ganin 'yan Najeriya suna biyan kuɗin wutar da s**a yi amfani da ita kaɗai.
Ministan ya ƙara da cewa gwamnatin tarayya za ta ci gaba da nazarin ƙarin hanyoyin da za su kare masu ƙaramin ƙarfi da marasa galihu daga duk wani nauyi, tare da tabbatar da cewa bangaren wutar lantarki ya samu tsarin kuɗaɗen da zai sa ya dore.
A cewarsa, gyaran da ake yi wa fannin wutar lantarki ba magana ce ta siyasa ko yaƙin neman zaɓe ba, illa aiwatar da tsare-tsare cikin tsari, haɗin kai da kuma auna sakamakon da ake samu.
Ya ce za a auna nasarar gyaran ne da irin sauyin da 'yan Najeriya za su gani a rayuwarsu ta yau da kullum.
Ministan ya ce burin gwamnatin tarayya shi ne samar da ingantacciyar wutar lantarki da za ta wadatar da gidaje, ta bunƙasa masana'antu, ta jawo masu zuba jari, tare da tabbatar da cewa kowane ɗan Najeriya ya amfana da ingantaccen tsarin samar da wutar lantarki.
31/07/2026
Da Dumi-Duminsa: Kasar Iran Ta Kai Hari Kan Sansanin Sojin Amurka Na Isa Air Base a Bahrain
Rundunar sojin Iran ta sanar a ranar Alhamis cewa ta kaddamar da hari kan kadarorin sojin Amurka da ke sansanin jiragen sama na Sheikh Isa Air Base a ƙasar Bahrain, kamar yadda kafafen yaɗa labaran gwamnatin Iran s**a ruwaito. Rahotanni sun bayyana cewa harin na daga cikin martanin Iran ga hare-haren da take zargin Amurka ta kai mata. Har zuwa yanzu, ba a samu cikakken bayani daga hukumomin Amurka ko Bahrain kan girman barnar ko asarar da harin ya haifar ba.
31/07/2026
Amurka da Saudiyya sun kai hare-hare kan sansanonin mayakan Iraki Masu Goyan Bayan Iran
Rundunar sojin Amurka ta tabbatar da cewa, tare da hadin gwiwar sojojin Saudiyya, ta kai hare-hare kan wasu sansanonin kungiyoyin gwagwarmaya a kasar Iraki da sanyin safiyar Laraba.
Ma'aikatar Tsaron Saudiyya ta ce an gudanar da hare-haren ne cikin hadin gwiwa da Rundunar Tsakiyar Sojin Amurka (CENTCOM), inda aka kai farmaki kan wasu wuraren da kungiyoyin mayaka ke amfani da su a Iraki.
Rahoton ya ce hare-haren sun kasance wani bangare na matakan soji da kasashen biyu ke dauka kan wuraren da suke zargin kungiyoyin mayaka ne ke amfani da su.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the business
Telephone
Website
Address
Maiduguri
Alerts
Be the first to know and let us send you an email when ISAH Muhammad ADAM posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.