Logic Tech
Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Logic Tech, Blogger, Tudun Wada.
Yadda ake Gane Fake Website
22/08/2026
Yadda Shafin Google yake a shekarar 1997
15/08/2026
Ɗan Arewa Ya Ƙirƙiri VS Code Extension da Ke Ba da Damar Yin Coding da Harshen Hausa
Wani matashi ɗan Arewa, Ibrahim Bashir Yahaya, mazaunin Zariya, ya ƙaddamar da wata sabuwar VS Code Extension da ke ba masu amfani damar rubuta code da amfani da kalmomin Hausa.
Wannan sabon aiki na da nufin sauƙaƙa koyon programming ga masu amfani da harshen Hausa, musamman ɗalibai da masu koyon fasahar kwamfuta.
Ɗaya daga cikin muhimman abubuwan da extension ɗin ke da su shi ne damar sauya code daga Turanci zuwa Hausa da kuma daga Hausa zuwa Turanci, cikin sauƙi.
A halin yanzu, extension ɗin na goyon bayan harsunan programming guda biyu, wato Python da Rust, yayin da ake shirin ƙara wasu harsunan programming a nan gaba.
Ibrahim Bashir Yahaya, wanda ya ƙirƙiri wannan aikin, masani ne a fannin gine-ginen manhajoji da na'urori masu sarrafa kansu (Robotics), kuma ya bayyana wannan aikin a shafinsa na Facebook.
Wannan na daga cikin ƙoƙarin amfani da harshen Hausa wajen faɗaɗa damar samun ilimin fasahar zamani da kuma ƙarfafa masu amfani da Hausa su shiga fannin programming da software development.
20/07/2026
20/07/2026
BANBANCI TSAKANIN GEOBOOK DA CHROMEBOOK COMPUTER.
A kwanakin nan, mutane da dama suna rikicewa wajen banbance GeoBook da Chromebook. Duk da cewa suna k**a da juna ta fuskar girma da kuma farashi, akwai babban banbanci a Specifications, Operating System, da kuma irin ayyukan da kowacce kwamfuta aka ƙera ta domin gudanarwa.
1. Chromebook:
Chromebook computer ce da aka ƙera domin amfani da ChromeOS, wato Operating System na kamfanin Google.
An ƙera ta ne musamman domin gudanar da ayyukan da s**a shafi Internet da Cloud Computing, k**ar:
✔️ Bincike a Google (Google Search)
✔️ Amfani da Gmail
✔️ Google Docs, Sheets da Slides
✔️ Kallon a YouTube
✔️ Online Learning da Virtual Meetings
✔️ Amfani da wasu Android Apps
Yawancin Chromebooks, musamman waɗanda basu da damar Installing Windows, basa iya daukar manyan Windows Applications k**ar Adobe Photoshop, CorelDRAW, AutoCAD, da sauran software da aka ƙera musamman domin Windows.
2. GeoBook
GeoBook kuwa computer ce da ke amfani da Windows Operating System, k**ar Windows 10 ko Windows 11. Wannan yana nufin tana iya gudanar da yawancin Windows Applications, gwargwadon ƙarfin Hardware Specifications ɗinta.
Ana iya amfani da ita wajen:
✔️ Microsoft Office (Word, Excel da PowerPoint)
✔️ Internet Browsing
✔️ Online Classes da Virtual Meetings
✔️ Basic Programming
✔️ Basic Graphic Design
✔️ Accounting Software
✔️ Ayyukan ofis da na makaranta
Sai dai, saboda yawanci tana zuwa da 4GB RAM da 64GB ko 128GB SSD, ba'a ƙera ta domin gudanar da manyan ayyuka masu buƙatar ƙarfi k**ar Professional Video Editing, Advanced 3D Design, Software Development mai nauyi, Virtualization, ko manyan PC Games ba.
Wacce ta fi dacewa da kai?
✅ Idan buƙatarka ita ce karatu, amfani da Google Apps, bincike a Internet da sauran ayyukan Online, to Chromebook za ta iya biyan buƙatarka.
✅ Idan kuma kana son computer da zaka riƙa amfani da Microsoft Office da sauran Windows Software, to GeoBook ita ce zaɓin da ya fi dacewa da kai.
01/07/2026
TABBAS HAKA TAKE
A yawancin shaguna da gidaje a Najeriya, CCTV Camera ana amfani da ita ne kawai domin ta ɗauki bidiyo. Idan aka yi sata ko wata barna, sai a koma a duba abin da ya faru.
Amma yanzu fasaha ta ci gaba sosai. Sabbin AI Smart CCTV Camera ba wai bidiyo kawai suke ɗauka ba, suna iya gano haɗari tun kafin ya faru.
Idan camera ta ga wani mutum ko wani motsi da ba ta saba gani ba, nan take za ta aika saƙo zuwa wayarka. Haka kuma za ka iya kallon abin da ke faruwa kai tsaye (Live Video) domin ka ɗauki matakin gaggawa.
Wannan tsarin yana amfani da AI Smart IP Camera, wadda ake haɗawa da internet ta hanyar Wi-Fi ko Ethernet. Camera ɗin tana da fasahar AI da ke iya bambance mutum, mota, dabba, ko duk wani motsi da ba a saba gani ba.
Ba camera kaɗai ake amfani da ita ba. Ana kuma haɗa wasu na'urori k**ar:
Motion Sensor – yana gano idan wani ya kusanci gidanka ko shaganka.
Door Sensor – yana gano idan an buɗe ƙofa ko ana ƙoƙarin b***e ta.
Glass Break Sensor – yana gano idan an fasa gilashin ƙofa ko taga.
Dukkan waɗannan na'urori suna aiki tare da wata na'ura ta tsakiya (Control Hub ko NVR), wadda ke sarrafa tsarin gaba ɗaya.
Haka kuma ana haɗa tsarin da manhaja (App) a wayar Android ko iPhone. Da zarar AI ta gano wani abu da ake zargi, cikin daƙiƙu kaɗan za ta turo maka da saƙo (Notification).
Idan ka buɗe saƙon, za ka iya kallon abin da ke faruwa kai tsaye daga wayarka, ko da kana nesa da gidanka ko shaganka. Wannan yana ba ka damar ɗaukar matakin gaggawa kafin abin ya lalace.
A taƙaice: Sabuwar AI Smart CCTV ba ta tsaya kan ɗaukar bidiyo kawai ba. Tana taimakawa wajen gano haɗari da wuri, tana sanar da mai gida ko mai shago nan take, kuma tana ƙara kare rayuka da dukiyoyi.
19/06/2026
Wanda ya san wannan device din yayi mana bayani
31/05/2026
Shout out to my newest followers! Excited to have you onboard! Abubakar Sanusi Othman, Abubakar Danzaki, Sahabi Musa Mangafi, Ahmad Idris Garba, Mahmuda Chindo, Adamu Ahmad, Aminu Garba, Iliyasu Sabiu, Mohammed Ali, Abdurrahman Aliyu, Shamsu Hamza Hassan, Muhammed Sani Idris, Buhari Lawal, Ibrahim Musa Naibi, Sadik Sadik, Jamilu Ibrahim, Shaibu Shaibu, Salihu Bununu, Aliyu Abdullahi
Yadda Ake kare kai daga masu kwacen Whatsapp
27/05/2026
This is my real face!
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the business
Telephone
Website
Address
Tudun Wada
Alerts
Be the first to know and let us send you an email when Logic Tech posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.