Taskar Arewa TV

Taskar Arewa TV

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Taskar Arewa TV, Video Creator, Wuse.

Taskar Arewa TV dandali ne na yada sahihan labarai, al'adu, ilimi, da abubuwan da s**a shafi ci gaban al'umma, domin isar da muryar Arewa zuwa ga duniya baki ɗaya.

12/08/2026

WANNAN TASHIN HANKALI DA ME YAYI K**A: An kira ni aka sanar da ni cewa abokina rasu a wannan yammacin.

Abin mamakin shi ne, yana cikin ƙoshin lafiya kafin wannan lamari. Amma ranar Talata aka garzaya da shi asibiti.

Naje na duba Shi ranar Laraba, sai na same shi yana numfashi da ƙyar, kuma hawan jininsa ya yi matuƙar tashi. Daga nan ya ba ni labarin abin da ya faru.

gwajin DNA na ’ya’yansa biyu da matarsa.

Amma sakamakon ya zo da abin da bai taɓa zato ba: an ce yaran biyu ba ’ya’yansa ba ne.
Ɗayan yana SS3, ɗayan kuma JSS2.

Wannan labari ya girgiza shi matuka.

Daga bisani, lafiyarsa ta ƙara tabarbarewa, har aka rasa shi a wannan yammacin. 😢💔

Taskar Arewa Tv

26/06/2026

Breaking news!!! Breaking news!!!

English version:
Chief of Staff to President Bola Tinubu, Hon. Femi Gbajabiamila, has said the Federal government will review the minimum wage of government workers to meet up with the current economic situation when the time comes.

Hausa version:

Shugaban Ma'aikatan Fadar Shugaban Ƙasa ga Shugaba Bola Tinubu, Hon. Femi Gbajabiamila, ya ce Gwamnatin Tarayya za ta sake duba mafi ƙarancin albashin ma'aikatan gwamnati saboda ya dace da halin tattalin arziƙin da ake ciki a wannan lokacin..

Taskar Arewa TV

Follow, like, comment and share

26/06/2026

Fitacciya a Masana'antar Kannywood, Aisha Humaira, ta bayyana cewar suna iya ƙoƙarinsu wajen isar da koken talakawa game da matsalolin tsaro dake addabar mutanen Najeriya zuwa ga gwamnatin ƙasa.

Da take bayani ga yan jaridu jim kadan bayan kammala addu'o'i na musamman kan matsalar tsaro wanda Triple R ta shirya, Humaira ta ce:

"Mutum ya na isar da sakon shi ne ta 'Media' saboda bashi da hanyar da zai taka ya je ya isar da sakon, mu kuma alhamdulillah muna da hanya, kuma muna zuwa cikin gida, muna isar musu da sakon, kuma daidai gwargwado muna ganin 'results', saboda suna sauraronmu, kuma suna bamu bayanai; wasu ma bayanan sirri ne wanda bai kamata mu zo mu faɗesu a 'public' ba. Kuma suna nuna mana irin nasarorin da aka samu a wasu ɓangaren game da halin da ake ciki."

Ta kara da cewa: "Shawarar da zamu basu (mutane) kowa ya ci gaba da addu'a, komai ya yi tsanani maganinshi Allah. Addu'ar nan kuma muma muna yi, muna yi a ɓoye yau kuma mun yi a bayyana ne."

Najeriya Ina Mafita?

Taskar Arewa TV

Photos from Taskar Arewa TV's post 26/06/2026

Tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo tare da tsohon gwamnan jihar Kano kuma ɗan takarar mataimakin Shugaban Ƙasa a jam'iyyar NDC Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, da kuma ɗan takarar gwamnan Kano na jam'iyyar Comrade Aminu Abdulssalam Gwarzo a daren jiya a Kano, a ziyarar aiki da Obasanjo ya kai jihar inda s**a hadu domin su gaisa tare da tattaunawa kan lamuran siyasa da ci gaban ƙasa.

Taskar Arewa TV

25/06/2026

Jaruma a Masana'antar Shirya Fina Finan Hausa Momee Gombe ta Gina Wa Maihaifata Masallacin Sadakatu jariya a Gare su

Meye Fatan ku.

Taskar Arewa TV

25/06/2026

Ana rade radin hassan makeup dan kasar nijar zai angonce da Tsohuwar matar gfresh daya saka wato Maryam nicky minaj.Inda muka jiyosu suna kiran sunan junansu da mylove babyna da kuma mijina

Meye raayinku?

Taskar Arewa TV

Photos from Taskar Arewa TV's post 19/06/2026

Mai Girma Tsohon Gwamnan Jihar Bauchi Mohammed Abdullahi Abubakar SAN Ya Gana da Mai Girma Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a Fadar Shugaban Kasa dake Babban birnin tarayya Abuja.

​Mai Girma Mohammed Abdullahi Abubakar, SAN, tsohon Gwamnan Jihar Bauchi kuma Dan Takarar Gwamna na jam'iyyar APC, a yau tare da Daya daga cikin jigogin jam'iyyar na jiha, Farfesa Muhammad Ali Pate, Mai Girma Ministan Lafiya da Jin Dadin Jama'a na Kasa, sun gana da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.

​Wannan muhimmiyar ganawa ta mayar da hankali ne kan batutuwan da s**a shafi kasa, ci gaban Jihar Bauchi, da kuma al'amuran da s**a shafi ci gaba da jin dadin jama'a. Haka kuma, tattaunawar ta mayar da hankali kan karfafa shugabanci na gari, inganta ci gaba mai dorewa, da kuma ciyar da tsare-tsaren da za su taimaka wa ci gaba da habakar Jihar Bauchi da ma Najeriya baki daya.

​Ganawar ta nuna irin jajircewar shugabannin wajen dorewar tattaunawa da hadin gwiwa domin mara baya ga sabon tsarin (Renewed Hope Agenda) da kuma burikan 'yan Najeriya baki daya.

​Shamsuddeen Lukman Abubakar
Ya rubuta cikin Harshen turanci.

Moh'd Alkasim ya fassara zuwa Harshen Hausa.

19/06/2026

Taskar Arewa TV

17/06/2026

Wani matashi mai suna Usman Officer ya bayyana cewa ya janye batun aurensa bayan iyayen budurwar da yake nema sun buƙaci a ƙara masa kuɗin sadaki daga naira 400,000 zuwa naira 600,000.

A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Usman ya ce bayan ya tara naira dubu ɗari huɗu domin kuɗin aure, an sanar da shi cewa sai ya cika da ƙarin naira 200,000 kafin a amince da auren.

Ya ce bayan ya samu kuɗin da ake nema, ya sake yin tunani kan lamarin, inda ya fara tambayar dalilin da ya sa ake matsa masa wajen ƙarin kuɗin.

Usman ya bayyana cewa daga bisani ya aika da wakilansa domin karɓo kuɗin da ya riga ya bayar, sannan ya yanke shawarar saka kuɗin cikin harkar kiwo maimakon ci gaba da shirye-shiryen auren.

A cewarsa, ya sayi awaki goma da tumaki goma da kuɗin naira dubu ɗari huɗu, yayin da ya ce zai yi amfani da ƙarin naira dubu ɗari biyu wajen gina rumfa domin dabbobin.

Ya kuma yi addu’ar Allah Ya sanya albarka a sabon kasuwancin nasa, tare da yi wa budurwar fatan samun wanda zai biya adadin kuɗin auren da iyayenta ke buƙata.

Sai dai babu wata sanarwa daga iyayen budurwar kan batun a lokacin haɗa wannan rahoto.

Taskar Arewa TV

17/06/2026

Shahararran mawaki a Kudancin Najeriya Davido ya bayyana cewa da Rarara na da Ilimi da sai ya tsaya ya yi magana dashi.

Ya Kuma bayyana Dauda Kahutu Rarara a matsayin sakarai wanda bai San komai ba. Hakan dai na zuwa ne sa'oi kadan bayan mawakin siyasa Dauda Kahutu Rarara ya caccaki Davido a shafinsa na Facebook.

Davido ya bayyana hakan ne a shafinsa na X Wanda a baya aka fi sani da twitter.

Me za ku ce?

Taskar Arewa TV

17/06/2026

LABARI DA DUMI-DUMINSA:An kai Hamza Darma kotu kan labarin da ya bayar na zargin rashawa a yayin nadin Sarkin Kano a mulkin Kwankwaso.

Labari Yana Nan Tafe.

Taskar Arewa TV

Want your business to be the top-listed Media Company in Wuse?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Website

Address


Wuse

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Taskar Arewa TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Subscribe

We will notify you when anything happens in Wuse.