KSTSB
RUKAYYA MUAZU DALHAT
21/04/2023
*Alk. Mal Dalhatu Muhammad * (Alkalin Makarfi)
Haifaffen Ang. Kakaki Zaria, kuma Jika wajen Malam Ibrahim Tsoho
Ya Rasu rana 10 ga Afrilu, 1956 (shekaru 67 da s**a wuce) a cikin watan Azumi a wancan lokacin.
Kafin Mutuwar shi, shine Alkalin Makarfi, kuma kwararren Tela ne, shi yasa ake mashi inkiya da Baban Keke, hamshakin Manomi kuma masanin Fikhu da Larabci. Yana cikin dai-daikun da s**a samu halartan aikin Hajji a Kasa. Kamar yanda yake masanin Larabci ne, ya kasance shi kanyi fassara a Fadan Zazzau Idan anyi baki Larabawa. Misali lokacin da shahararren Malamin nan wato Baba Ahmad Tudun wada Mahaifin su Dr Hakeem yazo Zaria shi ya Tattauna dashi a harshen Larabci a Fadan Zazzau.
Ya rasu kwanaki kadan bayan dawo wanshi Daga Kaduna wajen Hawan Daba da aka shirya wa Marigayiya Queen Elizabeth II A wata gajeruwan rashin lafiya a Garin Makarfi.
Ya rasu ya bar ‘Yaya Maza Takwas 8
1- Alk. Murtala Dalhatu
2- Alk. Bashir Dalhatu
3- Alk. Muazu Dalhatu
4- Alh. Maccido Dalhatu (Tsohon sakataren Gwamnatin kaduna kuma Tsohon Minister a lokacin Shonikan)
5- Alh. Hassan Dalhatu (Cigarin Zazzau)
6- Mal. Mustapha Dalhatu
7- Mal. Ibrahim Dalhatu
8- Prof. Abubakar Dalhatu
Allah Ya gafarta masu
Click here to claim your Sponsored Listing.
Website
Address
Zaria