Muhammad Ibrahim Matasa Mu Farka
Wannan shafi anyi shi ne domin wayar da kan matasa domin sune ƙashin bayan al-umma. Idan sun gyaru to al-umma ta gyaru
06/02/2026
Ya Allah ka amshi bakoncin mal Jameelu Kasa aljannce makomarsa damu baki daya
06/02/2026
Allah ya baiwa Malam Sa'a. Muna so a samu ire-iren malan su fito mu kuma zamu zabesu InshaaAllah
Tunda aka kafa tarihin Ƙasar nan ba'a taba ganin cikakken malamin Addini mai limin boko da addinin daya shiga siyasa ba sai a wannan ƙarnin, a ƙashin gaskiya muna maraba da wannan sauyi da aka samu. Idan Allah ya yawaita mana irinsu gaskiya abin murna ne da kuma ci gaba. InshaaAllah lokacin zaben gantalallu ya kusa zuwa karshe. Allah ka kawo sauyi mai albarka mai daurewa. Ya Allah kada ka k**a mu da laifin da wawayenmu suke aikatawa.
Rashin samun bayanai ke saka matasa su tsaya jira se gwamnati ko yan siyasa sun taimake su! Akwai matasan da suna gida amma sunfi karfin 10M a wata guda! Bincike zaka yi tuƙuru sannan ka zage dantse wajen aiki
Duk wanda Allah yake so ya shiryar dashi sai ya buɗe zuciyarsa domin ya amshi musulunci.
Matasa sune ƙashin bayan al'umma! Kada kayi sake wajen inganta rayuwarka
Idan kunce anyi mana ba dai dai ba wajen zaɓen waɗanda zasu wayar wa al'umma da kai akan sabon tsarin haraji sai ku tambayi kanku, manyanku suna ina aka ware ku? Da aka ware ku mene s**a yi a kai? Sabida haka ku sake shiri.
Babu Al'ummar da zata cigaba kota rabauta matukar matasan ta basa naiman ilimi da addini da kuma na sana'a tuƙuru dai dai da zamanin ta! Babu alkhairi ga matasan da basa neman ilimi
Babu alheri ga matasan da basu da sana'ar yi.
Babu alkhairi ga matasan da basu da aikin yi sai sata, ƙwace/fashi ko shaye shaye!
Ya ku al'umma ku tashi tsaye kudauki mataki akan gyara da saita lamarin matasa tun kafin su gagare kowa a gari ko anguwa.
Allah ka shiryatar mana da matasan mu ka gyara lamuranmu
Yana da matukar amfani mu kasance mutane masu hangen nesa da zurfin tunani sannan mu zamto tsintsiya ma daurin ki daya.
Al-ummar da kanta a hade yake to abu ne mai wuya kaga an keta tsakanin ta.
Menene dalilin da yasa kake/kike gani ya jawo mana rashin haɗin kai a yau?
26/09/2025
Wajibi ne ko wani matashi ya dage da neman na kan shi, kada ka taba tunanin roko ko daukar abin wani zai yaye maka talauci se dai ya sake jefa ka cikin kunci da tashin hankali.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Address
Zaria
Alerts
Be the first to know and let us send you an email when Muhammad Ibrahim Matasa Mu Farka posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.